Muhammad Maitela" />

Gwamnatin Borno Za Ta Baje Kolin Hotunan Masu Fyade

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana shirin ta na baje kolin sunaye da hotunan mutanen da aka kama da laifin fyade tare da na laifuka masu dangantaka da shi, kamar yadda kwamishiniyar a ma’aikatar mata a jihar Borno, Hon. Zuwaira Gambo.

 

Hajiya Zuwaira ta kara da cewa, sun kudurci wannan aniyar ne domin kowa ya san su tare da kunyatar fasu, kana hakan zai kasance kan-da-garki tare da jan hankali ga duk mai tunanin aikata laifin fyaden.

 

Haka zalika kuma, gwamnatin jihar ta bayyana shirin samar da dokokin kare hakkokin kananan yara (Child Right Act), bayan kammala zantawa da shugabanin addini da na gargajiya, a matsayin da su ke dashi cikin al’umma.

 

Ta yi wannan furucin ne a zantawa da manema, a babban dakin taro na gidan gwamnatin jihar ‘Multipurpose Hall’ a birnin Maiduguri, don tunawa da cikar Gwamna Farfesa Babagana Zulum, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki al’amarin kare hakkokin mata da yara da muhimmancin gaske a jihar.

 

Hajiya Gambo ta kara da cewa, tuni gwamnatin su ta dauki matakan hada hannu da makamai, sarakunan gargajiya tare da rundunar yan-sanda, wajen dakile yaduwar aikata ayyukan assha na fyade da manyan laifuka makamantan su, na cin zarafin mata.

 

“Kuma, za mu kokarin aiwatar da matsayar da gwamnatin tarayya ta dauka wajen daukar mataki ga dukan masu aikata laifin fyade, ta hanyar bayyana adadin su, sunaye, hotuna duk a waje guda domin dakile yaduwar aikata laifin. Kuma muna yin hakan ne tare da hadin gwiwar ma’aikatar al’amurran mata ta Nijeriya.”

 

“Sannan baya ga wannan kuma, dangane da fitar da hotunan ma su aikata laifukan aikata fyaden, haka kuma muna kokarin bai wa kananan yara kariya ta hanyar samar da dokar kare hakkokin su (Child Right Protection Act). Haka kuma mu na da al’amurra ma su muhimmanci dangane da malaman addini tare da sarakunan gargajiya. Kuma mun gano cewa jihar Kaduna ta na da yanayi makamancin namu, wanda saboda haka mun tura tawagar mu zuwa can tare da kokarin aiwatar da matakan yin amfani da fadakar wa ta hanyar malaman addini da sarakunan gargajiya.” In ji kwamishiniyar.

Exit mobile version