Madeleine Alingue, mai Magana da yawun gwamnatin Chadi, tace matakin yaci karo da kokarin Chadi na yaki da ta’addanci musamman a yankin Afirka ta Yamma da kuma duniya baki daya.
Gwamnatin Chadi ta bukaci shugaba Donald Trump da ya sake nazari kan matakin wanda tace ya shafi kimar Chadi da kuma dangantakar kasashen biyu.
Karkashin kwaskwarimar da shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa dokar hana shigar baki Musulmi kasar, ya kara Koriya ta Arewa, Benezuela da kuma Chadi, a matsayin kasashen da haramcin ya shafa yayin da aka janye Sudan daga cikin kasashe shiddan farko da suka share tsawon kwanaki 90, ana amfani da dokar a kansu.
Amurka ce ‘yan asalin wadannan kasashe suna kawo cikas ga sha’anin tsaronta, ko kuma gwamnatocin kasashen ba sa bai wa Amurka cikakken hadin-kai ta hanyar musayar bayanai da suka shafi matafiya.