Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Karamar Hukumar Mangu, biyo bayan wani rikici da ya balle a yankin.
LEADERSHIP ta tattaro cewa an kai hari unguwar Sabon Gari da ke garin Mangu a daren ranar Litinin, inda aka halaka wasu mutanen da ba a san adadinsu ba.
- Kisan Budurwa: Gwamnatin Adamawa Za Ta Rufe Otal 70
- Ba Irin Wannan Amurkar Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Suke Bukata Ba
A cewar wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnan, Gyang Bere ya fitar, ya ce gwamna Mutfwang ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro da abin ya shafa.
Ya bayyana mutanen da aikinsu ke da muhimmanci ne kawai za a bari su shiga karamar hukumar.
Sanarwar ta bukaci daukacin ‘yan mazauna Karamar Hukumar Mangu da su bi wannan umarni tare da taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanai don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Gwamna Mutfwang ya kuma jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa da wadanda suka jikkata.
Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
Ya ce gwamnatin za ta sassauta dokar hana fitar da zarar tsaro ya inganta a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp