Gwamnatin Habasha da ‘yan tawayen yankin Tigray sun ce a shirye suke su halarci tattaunawar sulhu da kungiyar kasashen Afirka ta gayyace su wadda za ta gudana a Afirka ta Kudu cikin watan nan don kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.
Mai bai wa Firaminista Abiy Ahmed shawara kan harkokin tsaro, ya ce gwamnati ta karbi goron gayyatar, yayin da jagoran ‘yan tawayen Tigray shi ma ya ce a shirye suke su aika da wakilansu zuwa tattaunawar sulhun.
- Mutum 30 Sun Nutse A Ruwa Yayin Tsere Wa Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Ambaliyar Ruwa: FRSC Ta Shawarci Matafiya Da Su Kauracewa Hanyar Lokoja Zuwa Abuja
Sai dai bangaren ‘yan tawayen na Tigray sun diga ayar tambaya kan tsarin da za a bi wajen ganawar, dai-dai lokacin da bangarorin biyu ke ci gaba da farmakar juna.
Fada ya sake barkewa tsakanin sojojin Habasha da ‘yan tawaye Tigray a karshen watan Agusta, lamarin da ya kawo karshen tsagaita wuta na tsawon watanni biyar tare da dakatar da kai agaji zuwa yankin Tigray, inda karancin abinci, da magunguna ya tagayyara miliyoyin mutane.
An shafe shekaru ana tafka ruwa n wuta a tsakanin bangarorin biyu.