Daga A.A. Masagala, Benin
Gwamnatin jihar Edo ta shirya tsare-tsare da hanyoyi, ta yadda za a samu damar bundasa harkar noma a fadin jihar a yayin da ta nuna cewa yana daga shirinta na samarwa dubban matasa ayyukan yi.
Kwamishinan sashin albarkatun noma na jihar Honarabul Monday Osagboro ya fadi hakan ne a wani taro da aka gudanar a Odeguete da ke daramar hukumar Obia ta gabas.
Kwamishina Monday Osagboro ya ba al’umman wannan yankin tabbacin cewa burin gwamnatinsu shi ne bundasa harkar noma ta hanyar tallafawa manoma da kayan aiki irin na zamani domin su samu damar tafiyar da kome a cikin saudi kuma a cewar kwamishinan gwamnatinsu a shirye take ta cigaba da samarwa matasa ayyukan yi a cikin jihar.