Gwamnatin jihar Yobe, a ranar Asabar ta bayyana cewa ta kashe sama da Naira biliyan biyu da digo tara (N2.9bn) wajen siyo takin zamani tare da raba shi ga manoman jihar; tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022.
Kwamishiniya a Ma’aikatar Noma da Albarkatun Kasa a jihar Yobe, Dakta Mairo Amshi, ita ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Damaturu.
- Mutum 10 Sun Bace A Ruwa Sakamakon Kifewar Wani Kwale-Kwale A Yobe
- Yadda Rugujewar Gadar Katarko Ta Katse Yobe Da Jihohin Borno Da Gombe
Dakta Mairo, ta ce gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan daya da digo biyar (N1.5bn) daga cikin jimlar kudin wajen siyan ton 3,000 na takin zamani samfurin NPK 20:10:10 a 2021.
Amshi ta kara da cewa yanzu haka ana ci gaba da rabon takin da kuma sayar da shi akan farashin naira 13,000 kan kowane buhu.
Bugu da kari kuma, ta ce gwamnatin jihar Yobe ta kashe Naira biliyan daya da digo hudu (N1.4bn) wajen siyo karin wasu ton 7,500 na NPK 15:15:15 a 2020. Wanda ta ce za a sayar wa manoman takin a kan Naira 5,000, kowace buhu, wanda kuma gwamnatin ta zabtare kashi 40 cikin 100 na farashin domin tallafa wa manoma.
Ta bayyana cewa a 2019, gwamnati ta kashe Naira miliyan 882 wajen siyo motocin noma 40, tare da rabasu bashi kan naira miliyan 11 ga manyan manoma a jihar; wanda za a biya cikin shekaru hudu.
A hannu guda kuma, Dr Mairo Amshi ta ce gwamnatin jihar Yobe tare da hadin gwiwar kungiyar Red Cross (ICRC) sun yi wa shanu, tumaki, awaki da karnuka sama da miliyan 1.2 allurar rigakafin cutuka daban-daban a fadin jihar.
Da ta juya a fannin bunkasa kiwo a jihar, Kwamishiniyar ta ce gwamnatin jihar Yobe ta ce sun samu goyon bayan likitocin dabbobi 135, kwararru a kiyon lafiyar dabbobi 47, a wuraren kiwon dabbobi biyar da kuma ofisoshin kula da lafiyar dabbobi 17 a fadin jihar.
Har wala yau, Dr Amshi ta ce jihar tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya (FMARD) sun kafa cibiyoyin bunkasa wuraren kiwon dabbobi a Badegana da Gurjaje.
Amshi ta ce tuni an samar da kayayyakin aikin gudanar da cibiyoyin wadanda sun hada da rijiyoyin burtsatse, madatsun ruwa, asibitin dabbobi, wurin ciyar da abinci, tafkunan kiwon kifi, hanyoyin shiga, wutar lantarki, ingantattun magunguna da wuraren tattara madara da sauransu.
Hakazalika, Kwamishiniyar ta ce gwamnatin jihar Yobe ta gina cibiyar gudanar da bincike da kiwon dabbobi (LIBC) a Nguru domin bunkasa kiwon dabbobin.
A fannin noman rani kuma, ta ce gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samu isasshen abinci, inda yanzu haka an samar da kadada (hectares) 2,000 na filayen noma a karkashin Shirin Noman LAVA a 2022 a jihar.
Haka kuma ta ce jihar Yobe tare da hadin gwiwar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sun kafa Cibiyar Binciken da Samar da Dabbobi ta Kasa (NAPRI) a Arewa Maso Gabas; a birnin Damaturu.
Kwamishinan ya kara da cewa jihar ta samu amincewar shiga shirin Gwamnatin Tarayya na Tallafin Dabbobin Dabbobi (Shirin L-Pres).