Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da sabon tsarin karantarwa da aka yi wa lakabi da “Nigeria Learning Passport’’ don bunkasa ilimi a matakin Firamare, Sakandare ga al’ummar jihar baki daya.
A yayin kaddamar da shirin a Kaduna, Kwamishiniyar Ilimi, Hajiya Halima Lawal, ta ce, an fito da sabon tsarin ne don samar da ingantaccen ilimi kamar yadda ake gudanarwa a sassan duniya.
- 2023: INEC Ta Kara Wa’adin Ranakun Yin Katin Zabe
- Ko Kun San Dakin Ibadar Aljannar Duniya Na Kasar Sin?
An samar da shirin ne don kara inganta harkar ilimi ga yara ‘yan firamare da sakandire a sassan jihar.
Shirin dai ya samu albarkacin ma’aikatar ilimi ta tarayya an kuma samar da shi ne don kulle ratar da ake samu a tsakanin al’umma wajen samun ingantacen ilimi.
A jawabinsa Mista Francis Elisha, wanda shi ne wakilin majalisar dinkin duniya na (UNICEF) ya ce annobar Korona ce ta tilasta neman hanyoyin cigaba da karantar da yara a lokacin da sake fuskantar kulle, ya kuma yi alkawarin tallafa wa shirin musamman ganin muhimancisa.