Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce, ta karbi manyan motocin yaki na musamman guda biyu da kuma karin ‘yansanda mutum 200 da suka samu horo na musamman a rundunar ‘yan sandan Nijeriya inda aka turo su jihar.
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Lahadi.
- An Sako Ɗaliban Makarantar Kuriga Da Aka Sace A Kaduna – Uba Sani
- ‘Yansanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindiga A Kaduna
Sani ya ce, “A yau, na karbi manyan motocin yaki guda biyu da kuma jami’an runduna ta musamman ta rundunar ‘yan sandan Nijeriya 200 da sufeto-Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun ya tura jihar Kaduna.
“Wannan wani shiri ne don a karfafa yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran nau’ikan laifuka.
“Wannan alkawari ne da ya cika. A ziyararsa ta karshe a jihar Kaduna, I-G ya yi alkawarin tura kayan aiki da ma’aikata domin karfafa yaki da nuna irin kwazon rundunar ‘yan sandan Nijeriya a jihar Kaduna.
“Muna godiya ga IG bisa irin goyon bayan da yake bai wa jihar Kaduna.
“Muna kuma godiya ga shugaban kasa kan irin gudunmawar da yake bayar wa a wannan mawuyacin lokaci da tarihin Nijeriya ta tsinci kanta, da kuma tabbatar da dawowar yaran makarantar Kuriga lafiya.” Cewar Sani.