Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Sanata Uba Sani a ranar 25 ga Oktoba, 2023 ya mika wa Shugaban Rundunar Sojin Sama (CAS), Air Marshal Hasan Abubakar takardun mallakar fili mai fadin hekta 43.746 da Jihar Kaduna ta ware wa Rundunar Sojojin Saman Nijeriya (NAF).
A sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ta ce, an tanadi Filayen ne don gina jerin gidaje da manyan jami’an Rundunar NAF zasu amfana bayan sun ajiye aiki.
- An Dawo Da Zirga-zirgar Jiragen Sama A Filin Jirgin Sama Na Kaduna
- Gwamnati Ta Samo Jarin Fiye Da Dala Biliyan 2 A Bangaren Wutar Lantarki
Samuel Aruwan, Shugaban Hukumar Babban Birnin Kaduna (KCTA) wanda ya wakilci Gwamna Sani a wajen taron mika takardar filin a hedikwatar NAF da ke Abuja, ya mika takardun filin ne ga shugaban sojin rundunar sama ta Nijeriya.
Gwamna Sani ya yabawa CAS bisa jagorancin sa da kuma rundunar NAF bisa kokari da sadaukarwa wajen ci gaba da yaki da ta’addanci da ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a jihar Kaduna da ma kasa baki daya.
Aruwan, wanda kuma shi ne mai kula da ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, ya tabbatar wa NAF kudirin gwamnatin jihar wajen inganta jin dadin ma’aikatan NAF da ma jami’an tsaro baki daya.
A nasa jawabin, CAS Hassan Abubakar ya yabawa Gwamna Sani da mutanen jihar Kaduna bisa irin wannan karamci da suka nuna, wanda a cewarsa hakan na nuni da dorewar kyakkyawar alaka tsakanin NAF da jihar Kaduna, tun a shekarun 1960.
Ya kara da cewa, dama jihar Kaduna, ta kasance gida ce ga babban base na NAF da ma’aikatan da ke bakin aiki da wadanda suka yi ritaya.
Da yake karin haske kan dalilin da ya sa rundunar NAF ke ba da fifiko wajen samar da Gidaje masu sauki ga ma’aikatanta da suka yi ritaya, Air Marshall Abubakar ya ce: “ Babban abun alfaharin NAF shi ne jajirtattun ma’aikatanta, in babu kwarin guiwa ga ma’aikata, duk nagartar makami ba zai yi tasiri ba.” Ya ba da tabbacin cewa, za a yi amfani da filin ta yadda ya dace.
Filin da aka ware mai fadin hekta 43.746 shi ne na farko cikin biyu da Gwamna Sani ya amince a mika wa sojojin NAF. Filin na biyu mai fadin hekta 44.894 za a sake mikawa NAF bayan kammala duk matakan da suka dace kamar yadda Hukumar Babban Birnin Kaduna (KCTA) ta bayyana.