Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 152 tare da lalata sansaninsu sama da 100 a karo na biyu da na uku a 2022.
Mista Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, yayin da yake gabatar da rahoton yanayin tsaro na kashi na biyu da na uku na shekarar 2022, ga gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai.
- ‘Gaskiyar Lamari Game Da Zargin Amfani Da Sinadarin Mercury A Rigakafin Yara’
- Xi Ya Yi Jawabi Ga Taron COP14 Kan Kiyaye Filaye Masu Dausayi
Aruwan ya ce dakarun kasa da ke kewayen jihar sun kashe ‘yan bindiga 152.
A cewarsa, an kashe ‘yan bindiga da dama a lokacin da aka kai farmaki ta sama kan sansanonin da aka gano, inda ya ce an kashe ‘yan bindiga 16 a wani rikici a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun, sannan an lalata sansanoni sama da 100 da ‘yan ta’adda suka mamaye.
Sai dai Aruwan ya ci gaba da cewa a cikin wannan lokaci jami’an tsaro sun ceto mutane 74 da aka yi garkuwa da su.
Ya kuma bayyana cewa, makaman da aka kama daga hannun ‘yan bindigar a cikin watanni shidan sun hada da, manyan bindigogi kirar GPMG guda biyu, AK-47 guda saba’in da hudu, AK-49 guda daya da kuma bindigogi kirar 06 guda tara.
Sauran sun hada da bindigogi masu wuta guda hudu, bindigogin fanfo guda hudu, bindiga g3 daya, bindigu na gida guda goma sha shida da kuma harsashi guda 5,398.
Ya kuma bayyana cewa an kwato haramtattun abubuwa daga hannun wadanda ake zargin.
Ya ce adadin haramtattun abubuwan da aka kama sun kai kilogiram 2,759.891 na tabar wiwi da miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa an samu ci gaba sosai a hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda ya ce kashe-kashe da garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya ragu matuka a kashi na uku, ya kara da cewa kokarin hadin gwiwar yana samun sakamako mai kyau.
Aruwan, wanda ya bayyana godiyarsa ga kwamandoji, hafsoshi da jami’an tsaro da suke aiki dare da rana don ganin an kyautata wa kowa, ya kuma bukaci jami’an tsaro da kada su yi kasa a gwiwa, wajen dakile hare-hare.