Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ayyana Laraba 4 ga watan Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai da harkokin ciki gida, Baba Halilu Dantiye, ya fitar a ranar Talata.
- Akwai Yiwuwar Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa Dubu 100 Ko 200 – NLC
- Tinubu Ya Maye Sunan El-Rufai, Ya Aike Wa Majalisa Karin Sunan Ministoci
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokutan bukukuwa domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sanya su cikin harkokinsu na yau da kullum.
Ya kuma bukaci jama’a da su rika yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba a Kano a Nijeriya baki daya.
Ya yi addu’ar Allah ya fitar da daukacin Musulmi a wannan lokaci mai wuya, ya kuma sa a dace a wannan damina.
Tuni dai bikin Maulidi ke ci gaba da kankanma a Nijeriya da ma duniya baki daya.