• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kano Ta Ba Iyalan Mamatan Wasanni Tallafin Naira Miliyan Ɗaya Kowane

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana bayar da tallafin Naira miliyan ɗaya ga kowanne iyali daga cikin iyalan ’yan wasa da jami’an da suka rasu a mummunan haɗarin mota yayin dawowarsu daga gasar National Sports Festival da aka kammala a Abeokuta, jihar Ogun.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai asibitin Nasarawa a Kano.

  • Mutane 21 Sun Mutu A Tawagar Ƴan Wasannin Kano A Hatsarin Mota
  • Ƙungiyar Gwamnoni Sun Yi Ta’aziya Kan Rasuwar Ƴan Wasan Kano 21

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa wannan rashi babban rashi ne ga jihar da Nijeriya gaba ɗaya, domin waɗanda suka rasu sun wakilci Kano da kwazo da kishin ƙasa, har ma da samun nasarori. Ya ce: “Wannan rana ce mai cike da baƙin ciki a tarihin wasanninmu. Wasu daga cikinsu sun dawo da lambobin yabo.”

Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai kakakin hukumar wasanni ta jihar, Ibrahim Galadima; mai ɗaukar hoto, Bilal Ahmad Salisu; direbobi, ma’aikatan lafiya, da ’yan wasa daga ƙungiyoyin kokawa da Dambe. Gwamnati ta kuma sha alwashin cewa za a raba kayan abinci da abubuwan buƙata ga iyalansu, tare da kulawa ta musamman ga waɗanda suka jikkata.

Kwamared Gwarzo ya kuma ziyarta asibitin Murtala Mohammed inda ake kula da wasu daga cikin waɗanda suka jikkata. Ya tabbatar musu da cewa gwamnatin Kano za ta tallafa musu har su warke, tare da yin addu’ar samun sauƙi da gafara ga mamatan.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
Manyan Labarai

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara
Manyan Labarai

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

October 20, 2025
Next Post
Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.