Gwamnatin Jihar Kano ta ba da gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno.
An gabatar da takardar cekin kuɗin ne ga Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ta hannun tawagar Kano yayin wata ziyarar alhini.
- Ambaliya: Gwamnatin Adamawa Ta Tallafa Wa Jihar Borno Da Naira Miliyan 50 Da Jiragen Ruwa 6
- NEMA Ta Ceto Mutane 400 Da Suka Maƙale Sanadin Ambaliya A Borno
Tawagar ta ƙunshi Kwamishina Baba Halilu Dantiye da Hajiya Amina Sani, tare da Mai Ba da shawara na musamman, Dr. Danyaro Yakasai, da suka wakilci Gwamna Abba Yusuf.
Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin haɗin kai wajen fuskantar irin wannan ibtila’i, tare da nuna jajensa ga waɗanda abin ya shafa.
A nasa bangaren, Gwamna Zulum ya nuna godiyarsa ga wannan tallafi, tare da alkawarin cewa za a yi amfani da kuɗin wajen taimakon waɗanda suka rasa muhallansu.
Ambaliyar ta tilasta wa ɗaruruwan iyalai barin gidajensu tare da haifar da mummunar barna, wanda ya sa aka fara haɗa tallafi cikin gaggawa.