Gwamnatin Kano ta tabbatar da ƙaruwar damuwa daga jama’a kan dawowar masu aiki da babura a matsayin haya, wato ‘Achaba’, a wasu yankunan birnin Kano, tana tabbatar da cewa jami’an tsaro sun fara ɗaukar matakai kan lamarin. Sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Lahadi ta tabbatar da cewa rahotannin sirri sun nuna cewa masu Achaba sun fara sake bayyana a wasu unguwannin cikin birni duk da dokar haramta su da ta daɗe tana aiki.
Waiya ya ce har ila yau an gano wasu da ba a san su ba suna shiga cikin al’umma suna amfani da babura a matsayin masu haya, musamman a yankunan kan iyaka da wasu makwabtan ƙananan hukumomi. Ya bayyana cewa gwamnati ta baza matakan tsaro a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa daga wannan lamari.
- Gwamnatin Kano Ta Musanta Jita-jitar Barazanar Tsaro A Jihar
- Barau Ya Gargaɗi Gwamna Abba Kan Siyasantar Da Batun Tsaro A Kano
A cewarsa, hukumomin tsaro sun karɓi dukkan kayan aiki da goyon bayan da suke buƙata daga gwamnati domin tabbatar da cewa suna gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa. Ya gode wa jama’a bisa wayar da kai da sanya ido, yana ƙara musu ƙwarin gwuiwar ci gaba da bayar da rahoton duk wani abin da suka ga ni da ba su yarda da shi ba ga hukuma mafi kusa da su.
LEADERSHIP ta tattaro cewa dokar haramta amfani da babura a matsayin haya ta shafe shekaru 12 a Kano saboda matsalolin tsaro. Bayyanar masu Achaba a wasu yankuna a kwanakin baya ta hana jama’a sukuni, saboda haka gwamnati ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakai domin kare lafiya da kwanciyar hankali a jihar.














