Shugaban Hukumar Dab’i da Tace Fina-Fina ta Jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakalla, ya ce gwamnatin Kano, ta kafa kwamiti na musamman domin tsaftace da kuma gyaran tarbiyya ga masu rawa a shafin TikTok da Instagram.
Afakalla, ya bayyana hakan ne a cikin shirin Barka da Hantsi na gidan rediyon Freedom da ke Kano.
- Ra’ayoyinku A Kan Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Na Wucin-Gadi
- Buhari Ya Ci Alwashin Kawo Karshen Lalacewar Layin Samar Da Wutar Lantarki Na Kasa
Ya ce gwamnati ba zata lamunci a bata tarbiyyar jama’arta ba, don haka ya zama wajibi ta dauki mataki a kan yadda ake kara samun masu rawar da ta saba da koyarwar addini da kuma al’ada a TikTok.
Har wa yau, ya ce gwamnatin ta kafa kwamitin karkashin hukumar tace fina-finan da kuma hukumar Hisbah domin dakile samun karuwar matasa da kan yi amfani da shafukan wajen yin rawar da ba ta dace ba.
Tik Tok da Instagram sun samu karbuwa matuka gaya, a wajen samari da ‘yan mata a Najeriya.
Kusan ana iya cewa ma su na daga cikin shafukan sada zumunta da ke samun karuwar masu amfani da su.
Haka kuma mafi yawan masu amfani da TikTok da Instagram matasa ne masu neman nishadi, wato masu nishandantar da mabiyansu.
Afakalla ya yi kira ga iyaye da sauran wadanda ke da hakkin tarbiyya da su mayar da hankali wajen sanya idanu a kan yadda ‘ya’yansu ke amfani da TikTok, Instagram da ma sauran shafukan sada zumunta.