Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kammala tsare-tsaren da suka wajaba a kokarin tunkarar matsalar ambaliyar ruwa, domin kauce wa asarar da aka tafka bara, wanda ta lalata amfanin gona mai yawa.
Sakataren Gwamnatin Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ne ya bayyana haka lokacin kaddamar da shirin ya she magudanun ruwa domin kawar da shara a Jihar Kano.
- Cire Tallafin Fetur: Gwamnatin Edo Za Ta Raba Wa Marasa Karfi Naira N20,000 Ga Duk Mutum Daya A Jihar
- Fasahar Aikin Gona Da Ire-Iren Hatsi Masu Inganci Na Sin A Bikin Baje Kolin Uganda
Dakta Bichi ya ce shirin hukumar kyautata yanayi na cikin tsare-tsaren matakan da Gwamnatin Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ke daukar domin kare afkuwar matsalar ambaliyar ruwa wadda Hukumar NIMET da NEMA da sauran hukumomin da ke da alaka da tunkarar matsalar ambaliyar ruwa. A cewar sakataren gwamnatin, an umurci ma’aikatar muhalli, ma’aikatar ayyuka, hukumar shara da hukumar gyara hanyoyi da su yi aiki tare dominn samun kyakkyawan sakamakon da ake fata.
Ya kara da cewa kungiyoyin sa kai da sauran masu taimakawa kokarin gwamnati na kara himma wajen tabbatar da gani Jihar Kano na kare sake fuskantar matsalar ambaliyar ruwa.
Sakataren gwamnatin ya bayyana gamsuwar gwamnatin Jihar Kano ga al’ummar bisa goyon baya da hadin kan da suke bai wa gwamnati.
Tun da farko, jami’in lura da Shirin SPC, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, yayin da yake zagawa da sakataren gwamnatin Kano gidan Baban Gwari da ke titin Katsina, ya tabbatar da cewa suna bukatar taimakon kayan aiki domin samun nasarar shirin, kuma ya bukaci hadin Kai da goyon bayan al’umma.