Gwamnatin Jihar Kano, ta raba Naira miliyan 12.7 ga mutane 281 da suka yi asarar dukiyoyinsu sakamakon gobara a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin Alhaji Adda’u Kutama, ya ce tallafin na nufin taimaka wa waÉ—anda gobarar ta shafa a kasuwannin ‘yan Katako da ke Dala da Bakin Kasuwar Asibiti a Gwarzo.
- Sin Ta Kafa Manya Da Matsakaitan Yankunan Ban Ruwa 7,300
- Manyan Makarantun Bauchi Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), ta tabbatar da cewa mutane 57 daga kasuwar ‘Yan Katako da 224 daga Bakin Kasuwa sun amfana bayan tantance irin asarar da suka yi.
Sakataren hukumar, Alhaji Isyaku Kubarachi, ya yaba wa ƙoƙarin gwamnan kuma ya gargaɗi jama’a su ɗauki matakan kare kansu daga gobara, musamman a lokacin hunturu .
Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana, Yusuf Muhammad, ya gode wa gwamnatin tare da alƙawarin amfani da kuɗin cikin hikima.