Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Gwamnatin Jihar Kano ta kashe kiyasin Miliyoyin Naira a matsayin tallafi ga Mabaratan da aka kama a manyan titunan Jihar Kano. Kamar yadda jami’ar yada labaran Ma’aikatar Mata ta Jihar Kano Bahijja Malam Kabara ta shaidawa LEADERSHIP A YAU.
Kwamishiniyar ma’akatar Mata ta Jihar Kano Dakta Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayyana Haka alokacin raba tallafin ga mabaratan a Kano. Kwamishiniyar ta ci gaba da cewa, an samar da kayan tallafin domin tallafawa Mabaratan domin dogaro da kansu.
Ta ce, mafi yawan wadanda aka kama akan titunanata ne da kananan yara wadanda suka tsunci kansu a halin bara sakamakon rashin samun isasshiyar kulawa.
Kwamishiniyar ta ce, kashin farko na wadanda suka amfana da tallafin an zabo su bayan tantancewa da aka yi masu da kuma bayanan da aka tattara.
Dakta Zahra’u ta kuma bayyana cewa, duk wanda aka sake kamawa daga cikin eadanda suka amfana da wannan tallafin za’a gurfana dashi gaban kotu domin girbar abinda ya shuka.
Kayan tallafin da aka raba sun hada da Firji, keken dinki, kayan abinci, injin bada hasken wutar lantarki, wake da sauransu.
Cikin wadanda suka amfana da wannan tallafi, Rukayya, Maryam da Aminu sun bayyana godiyarsa bisa wannan kabakin arzikin, sannan suka yi alkawarin daina bara a tsawon rayuwarsu.