Gwamnatin Jihar Katsina, ta ƙaddamar da wani shirin Rumbun Sauƙi, kan kuɗi Naira biliyan 4 da aka ƙirƙiro domin rage matsin tattalin arziƙi ta hanyar samar da kayan abinci da sauran masarufi kan farashi mai rahusa.
Mai ba wa Gwamna Dikko Radda, shawara na musamman kan harkokin tattalin arziƙin karkara, Yakubu Danja, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, inda ya jaddada cewa gwamnatin na ɗaukar matakan magance matsalar tsadar abinci da al’ummar jihar ke fuskanta.
- El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci
- Messi Zai Fuskanci Hukunci A Gasar MLS Ta Kasar Amurka
Ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin, za a buɗe shagunan tallafi a fadin jihar domin sayar da kayan abinci kamar su shinkafa da fulawa da garin masara da taliya kan ragin kashi 10 na farashinsu inda a matakin farko, za a buɗe kantunan a garin Katsina da Daura da Funtua, kana za a fadada shirin zuwa sauran yankunan jihar.
Shirin Rumbun Saukin zai fi bayar da da muhimmanci ne kan ma’aikatan gwamnati da dattijai masu shekaru 60 zuwa sama, inda kayan abincin za su kasance a nau’ikan ma’aunai daban-daban domin a dai-daita da bukatun iyalai da samun masu cin gajiya wanda za su yi rijista ta yanar gizo ko kuma ta cibiyoyin da aka tanada domin shirin.
Danja, ya ƙara da cewa burin gwamnati shi ne faɗaɗa shirin zuwa dukkan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar, tare jaddada himmatuwar gwamnatin Katsina na ci gaba da ɗaukar nauyin shirin domin rage matsin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp