Gwamnatin Jihar Katsina, ta sake jaddada matsayinta a kan bunkasa harkokin ilimi a fadin jihar baki-daya.
Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda ya bayar da tabbacin hakan ne a lokacin bikin yaye daliban jami’ar tarayya ta (FUDMA) 4,365 da suka kammala karatu a jami’a.
- ‘Yansandan Sun Kama Masu Laifi 130 A Watan Nuwamba A Katsina
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Asibiti, Makaranta Da Gidaje Ga Al’ummar Tudun Biri – Gwamnan Kaduna
A cewar gwamna Radda, gwamnatinsa wadda ta yi watanni 6 ta samu nasara a kan gyara makarantu da suka lakume sama da naira miliyan 200,000.
Ya kara da cewa, daukar malaman makaranta sama da 7,000 da kuma gyara makarantu 75 karkashin shirin bunkasa ilimin ‘ya’ya mata na AGILE, yana ci gaba da bunkasa bangaren ilimi a jihar.
Radda ya sake cewa, shawarar da gwamnatin jiha ta yi na sake gina makarantu 3 na gwaji zai taimaka wa daliban da suka fito daga gidajen marassa galihu.
Ya ce gwamnatinsa na kokarin tabbatar da maido da martabar makarantu da kuma yin alkawarin ci gaba da hadin gwiwa da dukkan abokan hulda domin samun nasara.