Gwamnatin jihar Katsina ta sake nanata kudurinta na cigaba da samar da dukkanin ababan da ake bukata, don cigaban manyan makarantun jihar.
Mai bai wa gwamna shawara akan ilimi mai zurfi ya bada tabbacin hakan a wajen wani taro na 30 da sashen ayyukan gonad a nazarin muhalli na kwalejin kimiyya ta Hassan Usman dake nan Katsina ta shirya.
Taron da ake gudanarwa a kowace shekara na da taken “shekaru 60 dda samun ‘yancin kan Nigeria kalubale da hanyoyin mafita da kuma rawar da imiyya da kere-kere zata taka.
Daga cikin kokarin da ake akan hakan kamar yadda Mal. Bishir Usman dama da gwamnatin jiha tayi na maye gurbinn malaman kwaleji.
Mal. Bishir Ruwan Godiya ya bukaci malamai das u cigaba da baiwa dalibai ingantaccen ilimi ta yadda zasu zama masu bada aiki ba masu neman aiki ba.
Tun farko shugaban makarantar Dr. Ibrahim Mudi Kurfi yace taron yazo akan kari dai dai da lokacin da kasar nan ke bukatar gudummuwar kimiyya da kere-kere.
A jawabinsa Galadiman Katsina hakimin Malumfashi mai Shari’a Sadik Abdullahi Mahuta mai ritaya ya yabawa malamai da gwamnati d masu bincike akan samar da horo ga maatsa masu tasowa.
A kasidar da ya gabatar Farfesa Habu Moh’d daga Jami’ar Bayero dake Kano ya zargi turawan mallaka akan rashin dora kasar nan kan turbar cigaban kimiya da kere-kere.
A wani labaran kuma gwamnatin jihar Katsina ta kara jaddada kudurinta na tallafa ma matan da matsalar yan bindiga ta shafa a kananan hukumomin da suke fama da matsalar tsaro a jihar nan.
Kwamishinan kula da harkokin mata ta jiha Hajiya Rabiya Muhammad Daura ta sanar da haka, a lokacin da take kaddamar da kasha na biyu na kayyakin jin kai da kungiyar kula da hukumar kula da karkokin kula da majalissar dinkin duniya . kungiyar nan ta UNIPA ta bayar da gudummuwa a farfajiyar ma’aikatar.
Hajiya Rabiya Muhammad Daura wadda ta yaba da kokarin kungiyar game da tallafin da ta baiwa mata wadanda matsalar harin ’yan bindiga ya shafa, tace tallafin zai tallafa ma kokarin gwamnati.
Kwamishinar ta tunaso cewa kungiyar ta bayar da gudumuuwar irin wadannan kayayyakin ga mata marassa karfi a jihar nan.
A wani jawabin Marabci Babban Sakatare na ma’aikatar Alh. Lawal Matazu wanda ya nuna godiyarshi ga kungiyar game da gudummuwar, ya bukaci sauran kungiyoyi masu zaman kansu da suyi koyi da kngiyar.
Ya kuma yi kira ga wadanda suka amfana da su yi kyakkyawan amfani da kayayyakin.
A madadin wadanda suka amfana Baraka daga kauyen Dankar a karamar hukumar Batsari da Amina Abdullahi duk daga karamar hukumar ta Batsari sun gode wa kungiyar game da tallafa masu. Sannan kuma sai suka bayar da tabbaci na yin kwakkyawan amfani da kayayyakin.