Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin mukaddashin gwamnan jihar, Malam Farouk Lawal Jobe, ta sassauta dokar hana yawon dare wanda ta sanya sakamakon zanga-zangar matsin rayuwa.
Yanzu haka dai gwamnatin ta bayyana cewa an sassauta dokar daga karfe 7 na dare zuwa 7 na safe, inda aka bai wa jama’a damar yin zirga-zirga daga karfe 5 safe zuwa karfe 10 na dare.
- Jami’in MDD Ya Yaba Da Samar Da Fasahar Juncao Don Bunkasa Tattalin Arziki Da Samar Da Ayyukan Yi A Afirka
- Ba Ni Da Burin Da Wuce Ziyarar Kabarin Manzon Allah – Fauziyya Sani
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari, ya fitar ta ce hakan ya biyo bayan gamsuwa da yanayin tsaro da aka samu saboda aka sasanta dokar.
Haka kuma sanarwar ta yaba wa yadda jami’an tsaro suka gudanar da aikinsu, da kuma yadda al’umma suka bada hadin kai a daidai lokacin da ake ƙoƙarin kwantar da tarzoma.
Mukaddashin gwamnan ya shawarci al’umma da su kasance masu bin doka da oda a harkokin su na yau da kullum.