Daga Sagir Abubakar
A kokarin da ake na bunkasa bada sana’o’in hannu a Jihar Katsina, za a gina kwalejin bada horo a kan sana’o’i a garin Majigiri yanki karamar hukumar Mashi.
Wanda zai gina kwalejin kuma memba mai wakiltar karamar hukumar Mashi da Dutsi a Majalisar Wakilai ta kasa, Hon. Mansir Ali MAshi, y ace kwalejin za a hada ta da kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina.
Kamar yadda ya ce, babban muhimmancin gina kwalejin a Majigiri shi ne domin bada dama ga matasan da suka fito daga yankunan kananan hukumomin Mashi da Dutsi da Daura da Kaita da Jibia da Mani su samu horo a kan sana’o’i wanda zai taimaka musu su tsaya da kafafuwansu, su zama masu dogaro da kansu.
Ya kara da cewa za a samu kudaden da za a gina kwalejin daga albashinsa na wata-wata da alawus. Mansir Ali Mashi ya kara da cewa wannan shiri bai tsaya nan ba kawai har matukar rayuwarsa zai ci gaba da tallafama matasan wannan yanki na Mashi da Dutsi da ma dukkanin al’ummar wanan yankin muddin yana da rai. Dan majalissar ya sha alwashin taimako ba ma sai in yana bisa wani mukami ba saboda yankin su ne.