Gwamnatin Katsina Za Ta Kirkiro Hukumar Jin Ra’ayin Jama’a

Kwamitin Tsaro

Daga Sagir Abubakar

Gwamnatin jihar Katsina na shirin kafa wata hukuma da zata kula da bukatin mutane masu bukata ta musamman a jihar.

Mai taimakama gwamna na musamman a kan lamurran mutane masu bukata ta musamman Alh. Ya’u Rufa’i Zakkaya bayyana haka yayin da yake jawabi ga mutane masu bukata ta musamman da suka fito daga yankunan kananan hukumomi sha daya (11) na shiyyar dan majalisar dattawa ta Funtua.

Mai bada shawara ta musamman din ya gana da tawagar ne a makarantar dake Malumfashi.

Alh. Ya’u Zakka yace gwamnati mai ci yanzu ta gwamna Aminu Bello Masari tana sane da kokarin da mutane masu bukata ta musamman sukayi a lokacin zabe.

Ya bayyana cewa batutuwan da suka shafi bunkasa rayuwar mutane masu bukata ta musamman zasu samu kyakkyawar kulawa daga gwamnati.

Don haka, mataimakin na musamman din yayi kira ga mutane masu bukata ta musamman dasu tallafama manufofin gwamnati ta hanyar tura ‘ya’aynsu zuwa makarantu.

Ya tabbatar da cewa ofishinsa zai cigaba da yin dukkan mai yiwuwa domin tallafama rayuwar masu bukata ta musamman.

A jawabin maraba, shugaban makarantar kurame ta gwamnati dake Malumfashi Malam Halliru Dogo ya godema mai taimakama gwamnan na musamman akan ziyarar wanda ya bayyana a matsayin irinta ta farko.

A lokacin ziyarar rangadin, mai ba gwamnan shawara ta musamman akan sha’anin masu bukata ta musamman ya bada tallafin kekuna ga dalibai guda biyu (2) ‘yan firamare da kuma allon rubuto fari ga makarantar.

An gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da cigaba mai dorewa a jiha dama kasa baki daya.

Exit mobile version