Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da sayen babura 700 da kuma motocin Hilux guda 20 a matsayin sabon mataki na yaƙi da ta’addanci, satar mutane da sauran ayyukan laifi a faɗin jihar.
Wannan amincewa ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 12 da aka gudanar a gidan gwamnati, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda.
- Dikko Radda Ya Bai Wa Gwarazan Hikayata Kyautar Kudi
- ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro
Kwamishinan Tsaron cikin gida Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa, ya shaida wa manema labarai bayan taron cewa, matsalar yanayin ƙasa a Katsina na daga cikin dalilan da suka sa aka yanke shawarar sayen baburan, domin akwai ƙauyuka da dama da motoci ba sa iya isa.
Ya ce gwamnati ta ɗauki tsaro da muhimmanci a matsayin abu na farko, na biyu da kuma na uku, tare da tabbatar da cewa za ta tunkari matsalar tsaro gaba ɗaya. Haka kuma, an amince da sayen kayan aikin tsaro na zamani da za su tallafa wa rundunar Katsina State Community Watch Corps tare da haɗin gwuiwar DSS da sauran hukumomin tsaro.
Dakta Danmusa ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da sayen motocin bindiga masu ƙarfi guda takwas na Toyota Land Cruiser (Buffalo) domin ƙara karfin runduna a yankunan da suka fi fama da hare-haren ƴan bindiga. Ya roƙi al’umma da su ci gaba da tallafa wa gwamnati ta hanyar addu’o’i da haɗin kai, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar dawo da zaman lafiya na dindindin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp