Gwamnatin  Kebbi Ta Karama Shugaban ofishin NIS Mai Kula Da Fasfo A Kebbi 

NIS

Daga, Umar Faruk Birnin-Kebbi,

A jiya ne ofishin sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Babale Umar Yauri ya aike da takardar Karamawa ga DCI Sabo  Mohammed shugaban ofishin NIS mai Kula da bada fasfo don tafiye-tafiye zuwa  kasashen waje na jihar  Kebbi kan irin kakorin da ya keyi na tabbatar da cewa cikin, awa 24 ko 48 an bada fasfo ga duk wanda ya nema cikin sauki batare da wani bata lokaci ba a jihar kebbi.

Bayanin hakan yana kunshe a cikin takardar karama wa ta lamabar yabo da ofishin na sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Babale Umar Yauri ya sanya wa hannu. Inda aka bayyana cewa” tun lokacin da a ka samar da ofishin NIS mai Kula da bada fasfo a jihar ba a taba samun shugaba wanda ke bada fasfo a cikin  awa 24 ko 48 sai DCI Sabo Saidu Mohammed wanda al’ummar jihar da kuma manyan jami’an gwamnatin jihar na cike da  murna da farin ciki kan irin wannan jajirtacen shugaba da hukumar NIS ta kasa ta turo a jihar ta Kebbi, inji takardar Kamara wa daga  ofishin sakataren gwamnatin jihar Kebbi”.

Bugu da kari takardar ta ci gaba da bayyana ce” a shekarun baya al’ummar jihar Kebbi na fama da matsalar samun fasfo wanda har sai sun tsallaka zuwa makotan jahohi kafin samun fasfo musamman a lokacin zuwa hajji jama’a na shan wahala,  amma zuwa DCI Sabo Saidu Mohammed matsalar ta kare har ma da yanayin mu’amalar jami’an ofishin na NIS mai Kula da bada fasfo ga al’ummar jihar Kebbi ya chanza domin jama’ar jihar sai san barka suke yi kan samun irin wannan shugaba a ofishin na NIS a jihar ta Kebbi.

Daga nan sakataren gwamnatin jihar ya kara bayyana cewa” DCI Sabo Saidu Mohammed ya kawo chanji da kuma sauyi a ofishin bada fasfo na hukumar NIS ta jihar sosai, haka kuma yanayin aiki sa a jihar kebbi ya nuna cewa shi mai kwazo ne har ma da jami’an da ya ke aiki dasu a jihar.

A karshe, ya yi  kira DCI Sabo Saidu Mohammed da jami’an ofishinsa da kuma hukumar NIS da ta turo shi  jihar kebbi da su ci gaba da irin wannan aiki na tabbatar da cewa al’ummar jihar Kebbi da  na kasar nan sun samu fasfo cikin awa a 24 ko 48 wannan ba karamar nasara ba ce aka samu.

Exit mobile version