Gwamnatin Jihar Kogi ta zurfafa haɗin gwuiwa da hukumomin tarayya da kuma masu zuba jari na ƙasashen waje domin mayar da noma ginshiƙin a tattalin arziƙin jihar, da tabbatar da samar da wadataccen abinci da kuma fitar da amfanin gona zuwa ƙasashen waje.
Kwamishinan Noma da tsaro na abinci, Timothy Ojomah, ya bayyana haka a yayin ziyarar duba wata gona a Geregu, ƙaramar hukumar Ajaokuta, tare da ƙwararru da masu zuba jari, inda suka tattauna kan damar noman zamani da faɗaɗa kasuwa. Ya ce wannan tsari yana daidai da hangen nesa na Gwamna Usman Ododo wajen ƙarfafa manoma, samar da aiyukan yi, da kuma gina tattalin arziƙi mai ɗorewa.
- NGF Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Gonaki A Kogi, Ta Tsaida Aiyuka A Legas
A nasa jawabin, Mai ba wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin noma, Mathew Ajayi, ya ce haɗin gwuiwar ta yi daidai da shirin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da tsaron abinci da rage dogaro da shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje. Ya ce an fi karkata hankali kan shinkafa, da masara, da waken soya da wasu amfanin gona da za a iya fitarwa zuwa ƙasashen waje.
Shugaban Hukumar Musayar Amfanin Gona ta Jihar Kogi, Victor Omofaiye, ya bayyana cewa hukumar za ta tabbatar da farashi mai adalci da samun damar kasuwannin waje ga manoma. A gefe guda kuma, Daraktan Onida Agri, Israel Kidron, ya ce Kogi ta dace da noman zamani saboda ƙasar ta mai albarka ce da kuma wadataccen ruwa. Ya ƙara da cewa kamfanin zai taimaka wajen horas da manoma da kawo fasahohi na zamani domin inganta amfanin gona.
Wannan haɗin gwuiwa ana sa ran zai ratsa wasu ƙananan hukumomi a jihar, inda zai samar da ayyukan yi, da ƙarfafa manoma, tare da mayar da Kogi ɗaya daga cikin manyan jihohin da ke taka rawa wajen sauya fasalin noma a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp