A kalla mabarata da ke farace-farace kan titunan Illorin ne gwamnatin Jihar Kwara ta maida su zuwa jihohinsu na asali a cikin shekara guda da ya gabata.
Kwamishinan kula da jin dadi da walwalar jama’a, Misis Afolashade Opeyemi, ita ce ta shaida hakan a ranar Litinin a lokacin da take ganawa da ‘yan jarida kan aikace-aikacensu da ma’aikatar yada labarai ta jihar ke shiryawa a Illorin babban birnin jihar.
- Ibtila’in Mutuwar Almajirai A Kebbi…
- Gwamnatin Tarayya Ta Sa Almajirai Da Yara Fiye Da Miliyan 2 A Karatun Boko
Opeyemi ta ce mabaratan da aka kama da maidasu garuruwansu mafi yawansu sun fito ne daga jihohin Bauchi, Kano da kuma wasu jihohin da suke arewaci da suka barazana ga zamantakewa a cikin Illorin da kewayenta.
Ta ce, a lokacin da ake aikin kwasan mabaratan zuwa garuruwansu, an gano muggan makamai da suka hada da bindigogi, wukake, layu, “Bincikenmu ya nuna mana cewa masu aikata laifuka ne.”
Ta kuma kara da cewa akwai wasu masu tabin hankali biyar da gwamnatin jihar ta yi jinyarsu kafin maidasu zuwa garuruwansu.
Ta ce akwai kuma wasu muhaukata biyar da ke barazana ga kwanciyar hankalin birnin su ma an musu jinya a karkashin gwamnatin jihar, kuma an maidasu garuruwansu a Olorunda da ke jihar.
Ta ce, masu matsalar kwakwalwar an sallamesu daga asibiti bayan tabbatar da shawo kan matsalar rashin lafiyar nasu.
“An maidasu Akwa-Ibom da Kurus Riba inda suka fito tun da farko,” ta shaida.