Gwamnatin Jihar Legas ta rufe makarantar Redeemers da ke Ogba biyo bayan mutuwar wani dalibi yayin daukar darasin ninkayar ruwa.
Takunkumin ya biyo bayan mutuwar wani dalibi mai suna Chidera Eze, mai shekaru biyar a lokacin da ya daukar darasin ninkaya.
- Mutum 12 Sun Mutu Yayin Arangama Tsakanin ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Banga A Filato
- Hadarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 18 A Hanyar Ibadan Zuwa Lagos
Chidera da takwarorinsa sun ce suna wasa a kusa da tafkin a lokacin da ya fada ciki.
Lamarin ya faru ne a watan Mayu a gidan kula da lafiya na Ivory Coast da ke titin Ogundana, Ikeja.
Mahaifin marigayin, Anthony Eze, ya dora alhakin mutuwar yaronsa a kan sakacin jami’an makarantar.
A ranar Litinin, ma’aikatar ilimi ta ce makarantar Redeemers za ta ci gaba da kasancewa a rufe, har sai an gudanar da binciken da ake gudanarwa.
Wata sanarwa da kwamishiniyar ilimi, Folashade Adefisayo, ta fitar ta ce za a binciki ayyukan makarantar da kuma yadda jami’anta ke gudanar d ayyukansu dangane da matakan tsaro.
Ta ce binciken farko da ofishin tabbatar da ingancin ilimi ya gudanar ya nuna cewa har yanzu makarantar ba ta kammala rajista da gwamnatin jihar ba, don haka ba a amince da ita ba.
Kwamishiniyar ta shawarci iyaye da su bada hadin kai har zuwa lokacin kammala binciken.
“Ma’aikatar ta damu da lafiyar daliban, don haka akwai bukatar shiga tsakani”, in ji ta.