Zubairu M Lawal" />

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Dauki Mataki Kan Tsaftar Muhalli

Gwamnatin jihar Nasarawa za ta dauki matakin ba sani ba sabo kan masu bijirewa dokar shara da ake gudanarwa duk karshen wata.

Da ya ke jawabi ga manema labarai, Kwamishinan Ma’aikatan tsaftar muhalli da tsare – tsare na jihar Alhaji Musa Ibrahim, ya ce; Gwamnati ta tsayar da ranakun Asabar din karshen wata a matsayin ranar tsaftar muhali. Amma abin bakin ciki sai ka tarar da wasu suna karya doka suna fitowa sana’arsu ba tare da sun gudanar da share gidajen su ba.

Ya ce; tsafta tana da mahimmanci ga rayuwar al’umma saboda duk wasu cututtuka ana samun su ne daga kazanta.

Yanzu cututtuka suna dada  karuwa, ga cutar zazzabin cizon sauro ga na zazzabin Lassa wanda ake samu daga Bera da sauransu.

Idan mutane ba su tsaftace muhallin su ba me zai hana sauro su addabi gidaje da dakunan  kwana. Hakama Beraye za su samu guraren yawo suna neman abinci hakan zai sanya su shigo inda ake ajiyar abinci suna tsoma baki.

Ya kara da cewa ; Masu ababen hawa kamar ‘yan kabu -kabu da masu tukin mota su kasance masu kiyayewa su bi doka.
“Domin yanzun mun hada karfi da karfe da kowane bangare na jami’an tsaro da ma Shugabannin al’umma da na ‘yan kasuwa da na Direbobi da na ‘yan Achaba. Mu na aiki tare duk wanda aka kama ya saba doka akwai kotun tafi da gidan ka da za a hukunta shi.”

Exit mobile version