Gwamnatin Neja Ta Zartas Da Dokar Rataya Ga Masu Garkuwa

….An Nemi Sauran Jihohi Su Bi Sahu

Gwamnatin Neja

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Gwamna Abubakar Sani-Bello na Neja a ranar Juma’a ya sanya hannu kan dokar hukuncin kisa ta hanyar rataya ga barayin shanu, ‘yan fashi, masu satar mutane da masu kai rahoto ga ‘yan ta’adda a jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar 1 ga watan Yuli, Majalisar dokokin jihar Neja ta zartar da dokar da ke tsara hukuncin kisa ga masu kai rahoto, masu satar mutane, da barayin shanu a jihar.

Bello ya kara da cewa, an yi kwaskwarima a dokar musamman ta satar mutane da satar shanu ta 2016 don azabtar da masu kai rahoto da kuma duk wadanda ke da hannu wajen taimakawa da satar mutane da satar shanu a jihar.

Ya ci gaba da cewa, masu ba da bayanan da ke taimaka wa masu satar mutane yanzu za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya a bainar jama’a kamar yadda dokar jihar ta tanada.

“Doka a yanzu ta bayar da cewa duk wanda ya tunzura wani mutum ya yi garkuwa da mutum ko kuma ya sace shanu, ko kuma ya taimaka da gangan, ya taimaka ko kuma saukakawa ta kowane irin aiki na barin aiki ko aikata laifin satar mutane da ko satar shanu yana da laifi, kuma zai fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya a gaban jama’a,” in ji shi.

Gwamnan ya ce, matakin na ladabtarwa ya yi kyau ya zama dole idan aka yi la’akari da kalubalen tsaro da ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar jihar musamman ta kasa baki daya.

Ya yi magana akan ayyukan rashin kishin kasa na masu kai bayanai wadanda a cewarsa, sun ba da gudummawa wajen dakile kokarin da hukumomin tsaro ke yi na magance munanan ayyukan masu satar mutane da barayin shanu.

Ya yi nuni da cewa dokar yin garambawul din an yi su ne domin karfafawa da kuma karfafa kungiyar ‘yan sintiri na jihar don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a yayin da suke gudanar da ayyukansu na doka wanda zai taimaka wa kokarin jami’an tsaronmu na tarayya.

Gwamnan ya bayyana fatan cewa sanya hannu kan dokar hukumar kula da ayyukan majalisar jihar zai kara bunkasa ayyukan ‘yan majalisar tare da tabbatar da hadin kan da ke akwai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar.

Exit mobile version