Gwamnatin Jihar Neja ta kimtsa domin fito da wani tsarin ci gaba na shekaru 30 masu zuwa da za a aiwatar daki-daki har a cimma gaci.
Bologi Ibrahim, babban Sakataren watsa labarai na gwamna Mohammed Umaru Bago, shi ne ya sanar da hakan ta cikin sanarwar da ya fitar a garin Minna, ya ce, gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ganawa da babban daraktan Bankin AfDB a Nijeriya, Lamin Barrow, a ofishinsa da ke Abuja.
- Yanzu-yanzu: Gwamnan Neja Ya Mika Takardun Mika Gwamnati Ga Zababben Gwamna, Bago
- Barayin Mutane Sun Tura Mutumin Da Suka Sace Ya Sayo Musu Man Fetur A Neja
Ganawar wacce aka yi ta kan gina wata kyakkyawar alakar aiki tsakanin Bankin da Gwamnatin jihar domin kawo ci gaba a jihar ta hanyar gina makarantu, tsarin dakile zaizayar kasa, makamashi da sauran fannoni.
Gwamna Umaru Bago, ya ce, a karon farko Gwamnatin jihar za ta samar da filin noma mai girman hekta 100,000 domin gudanar da ayyukan noma, kana za a fito da tsare-tsaren kyautata harkar noma da makamashi.
Gwamnan ya bayyana cewa, jihar Allah ya albarkaceta da dumbin albarkatun kasa, don haka gwamnatinsa za ta nemi masu zuba jari domin tabbatar da jihar ta amfana da dumbin albarkatun da Allah ya huwace musu.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa jihar za ta yi duk mai yiyuwa wajen saukaka wa masu zuba jari hanyoyin da za su samu zuwa jihar gudanar da kasuwancin domin haka ta cimma ruwa.
Lamin Barrow ya ce, tabbas hadakar za ta taimaka wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar musamman a bangaren Ma’adinai.
Ya nuna kwarin guiwarsa na cewa Gwamnatin Bago tana da kwarewar da za ta iya cimma nasarorin kyautata rabon ribar demokradiyya ga al’umma ta yadda kowa zai mora.