• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Sakkwato Za Ta Binciki Harin Jirgin Soja Da Ya Kashe Mutane

by Sadiq
4 months ago
in Manyan Labarai
0
Gwamnatin Sakkwato Za Ta Binciki Harin Jirgin Soja Da Ya Kashe Mutane
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce za ta haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin bincikar dalilin harin jirgin saman yaki da aka kai wasu ƙauyukan jihar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10.

Harin ya faru ne lokacin da jirgin yakin ya kai farmaki a sansanonin ’yan ta’adda na Lakurawa, waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a jihar.

Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya tabbatar da mutuwar mutane a sakamakon harin jirgin yaƙi a ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar hukumar Silame.

Ya ce harin ya faru ne bisa kuskure.

Ba wannan ne karo na farko ba da ake samun kuskuren irin wannan farmaki ba.

Labarai Masu Nasaba

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

A watan Disamban 2023, irin haka ya faru a Tudun Biri, a Jihar Kaduna, haka kuma ya taba faruwa a jihohin Nasarawa da Adamawa.

’Yan Nijeriya suna ci gaba da nuna damuwa, inda ƙungiyar tuntuba ta arewa ta buƙaci a ɗauki matakin kare faruwar irin wannan kuskure a nan gaba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin, Lt. Col. Abubakar Abdullahi, ya ce sojojin suna aiki ne bisa bayanan sirri da suka samu.

Sai dai, ya nuna rashin jin dadi kan yadda ake yada labaran da ba su da tabbaci a kafafen sada zumunta.

A halin yanzu, mutanen ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa na cikin alhini kan mutuwar mutane 10, tare da fargabar abin da ka iya sake faruwa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Jirgin YaƙiSakkwato
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ya Kamata Wasu Kasashe Su Daina Goyon Bayan Masu Adawa Da Sin Dake Tayar Da Tarzoma A HK

Next Post

Mota Ta Kaɗe Masu Tattakin Kirsimeti 22 A Gombe

Related

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje
Manyan Labarai

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

6 hours ago
Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai
Manyan Labarai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

7 hours ago
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa
Manyan Labarai

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

15 hours ago
Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma
Da ɗumi-ɗuminsa

Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

19 hours ago
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

20 hours ago
Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kai Ziyarar Aiki Jihar Anambra

22 hours ago
Next Post
Mota Ta Kaɗe Masu Tattakin Kirsimeti 22 A Gombe

Mota Ta Kaɗe Masu Tattakin Kirsimeti 22 A Gombe

LABARAI MASU NASABA

Hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

May 9, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

May 9, 2025
AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

May 9, 2025
Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

May 9, 2025
Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

May 9, 2025
Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

May 9, 2025
Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.