Gwamnatin tarayya ta karyata labaran da ake ta yadawa ta kafar sadarwa ta zamani cewar gwamnatin tarayya ta soke jarrabwar WAEC da NECO wadanda aka yi a shekarar 2025 saboda abubuwan da aka yi wadanda suka sabawa dokokin jarabawar biyu.
A sanarwar da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta fitar makon daya gabata wadda kuma dauke da sa hannun darekta na ‘yan jarida da hulda da jama’a, Boriowo Folasade, ya sake ya bayyana rahoton, a matsayin wani abu ne da aka shirya shi, domin a tada hankalin al’umma da suka hada da dalibai, Iyaye, da jama’a baki daya.
- Edo Da Taraba : ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 31 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Bayan Musayar Wuta
- Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
Ma’aikatar ta tabbatar da cewa an kammala jarabawar WAEC ta shekarar 2025 cikin nasara ba tare da wata matsala ba,in da an hadu da wasu matsaloli amma an yi maganinsu da hukumar ita ta yi hakan.
Hakanan ma ta kara yin bayani cewar jarrabawar NECO da ana yin ta ba tare da wata matsala ba, a daidai lokacin da ake shi wannan jawabin babu wta matsalar da aka hadu da ita.
Ma’aikatar ta jaddada bata samu wani labara ba daga wani jami’inta ko rahoto daga hukumomin WAEC, da NECO ko kuma wata hukumar dangane da wani abinda aka yi daya sabwa doka lokacin jarrabawar.
Don haka nema tayi kira da jama’a kada suyi amfani da shi labarin daya zaman a kanzon kurege da ake ta yadawa,idan wani bayani suke bukata su tuntubi kafa da suka san ba zata yi zuki ta malle ba,ko kuma jami’an ma’aikatar ilimi ta kafar sadarwarsu ko kuma na, WAEC, da NECO.
“An ja hankalin ma’aikatar ilimi ta tarayya akan wani labara ko rahoton da ya karade kafafen sadarwa na zamani,inda aka yi maganar cewar ban soke jarabawar WAEC ta shekarar 2025 da aka yi saboda an samu laifin aikata magudi lokacin da ake yin ta.
“Ma’aikatar tace don haka tana sanar da jama’a cewa ta yi nesa da kanta,dangane da ita sanarwar ko labarin saboda kuwa ai na kanzon kurege ne inda ta kara jaddada: Jarabawar, WAEC ta shekarar 2025,an kammala ta cikin nasara ba tare da wata matsalar data gagara shawo kai ba,in banda wadansu ‘yan kananan laifukan da suka auku,wadanda kuma ita hukumar tayi maganinsu.
“Ita kuma jarabawar NECO ana yinta ba tare da wata matsala ba, ya zuwa kuma hali ko lokacin da ake ciki babu wata matsalar da aka fuskanta. Ma’aikatar ilimi ta tarayya bata samu wani sako ba a hukumance daga WAEC ko kuma NECO,ko kuma duk wata hukuma mai shirya jarabawa da ke nuna an samu aikata magudin jarabawa.”
Ma’aikatar har yanzu babu wani abinda daya tada mata hankali wanda ya wuce aikata lamurran da suka shafi jarabawa cikin gaskiya da rikon amana,da kuma kwanciyar hankali, tana aiki kafada da kafada da su hukumomin jarrabawar,domin a samu inganta yadda ake lura da sa idon dangane da yadda ake gudanar da jarabawar.
Daga karshe ma’aikatar ta kara jaddada ta sha alwashin yadda ake gudanar da jarabawar yayi daidai kamar yadda dokokin hukumar suka bayyana, na samun gaskiya kan duk wata jarabawar da ake yi a Nijeriya,don haka su hukumomin jarrabawar jarabawar abokan huldar ta ne da kuma aiki tare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp