Gwmnatin Tarayya ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da shugabanni a fannin masana’antu, da su gudanar da shugabanci na gari tare da tabbatar da bin ka’ida, musamman domin a kara a habaka arzikin da ke a cikin nahiyar Afirka.
A cewar Gwamnatin, ba za ta kwale masu zagon kasa ko masu wata manufa su tarwatsa masana’antar ba.
- Gwamnatin Tinubu Na Amfani Da Kuɗaɗen Tallafin Mai Don Ci Gaban Al’umma – Minista
- Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya sanar da haka a jawabinsa a taron kaddamar da baje koli na kasa da kasa IEEER da aka gudanar a Abijan, Babban Birinin Kasar Coded’boire.
Kazalika, Shetrima ya bayyana cewa, wasu masu sanya ra’ayin kashin kansu a fannin gudanar da masana’antu ne ke janyo akuwar kalubale ga fannin da kuma janyo haddasa aukuwar rikice-rikice a yankunan da ke da albarkatun danyen mai
Shettima ya ci gaba da cewa, “Ba zan rungume hannu mu kyale irin wadannan masu yiwa fannin na masana’antu, zagon kasa ba, musamman don kar su samu damar cika burinsu”.
Mataikin ya kara da cewa, domin a takawa irin wadannan masu zagon kasar birki ne, Nijeriya ta samar da wani tsari na musamman domin a bai wa yankunan da ake hakar ma’adainai na kasar kariyar da ta kamata, musamman don a kara habaka fannin na ma’adanan kasar.
Ya sanar da cewa, Nijeriya Allah ya albarkace ta da Gwal da ya kai kashi 40 a cikin dari a fadin duniya.
Kazalika, Shettima ya sanar da cewa, Nijeriya na da yawan mai da ya kai kashi 10 a ciin dari, tare da kuma albarkatun kasa kamar irinsucobalt da lithium.
Sai dai, ya bayyana cewa, akwai irin wadannan albakatun kasar da har yanzu, ba a riga an tono su ba.
Mataimakin ya kuma bayar da tabbacin cewa, Nijeriya za ta ci gaba kula da masana’antun kasar, musamman domin a tabbatar da bin ka’ida da yin hadaka a kan kayan da ake sarrafawa a cikin kasar nan.
Taken taron shi ne, “Samar da Tsare-Tsare domin a kara habaka kayan da ake sarrafawa da kuma kula da masana’antar samar da makamashi”.
Shugabani da suka fito daga kasashen Afrika da dama ne suka halarci taron domin su tattauna kan yadda za su lalubo da mafita a fannin kirkier-kirkire da kuma kara kula da fannin samar da makamashi.
A cewar Mataimakin Shugaban kasar ba wai kawai ana magana ne a kan albarkatun kasa ba, batun ya kuma hada da yadda za a inganta rayuwar alumma da kuma samar masu da turba mai dorewa.
Ya sanar da cewa, idan aka samar da tsare-tsaren da suka kamata da bin ka’ida da kuma tabbatar da gaskiya, za a iya samun damar bunkasa fannin samar da mai mai makon kawo rabuwar kawuna.
Shettima ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya a cikin sauye-sauyen da ta samar da ta kara habaka ayyukan Hukumar dake sa ido kan albarkatun ma’adanai ta kasa, wato NEITI.
Kazalika, Shettima ya bayar da tabbacin cewa, akwai bukatar kasashen da ke a nahiyar Afrika da ke fuskantar kalubale iri daya da su mayar da hankali wajen lalubo da hanyoyin magance kalubalen.
Mataimakin Shugaban kasar ya sanar da cewa, sake samar da sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi a kamfanin man fetur na kasa NNPCL a karkashin dokar da ke tafiyar da masana’antar sarrafa man fetur ta 2021, hakan ya sanya kamfanin ya mayar da hankali wajen hada-hadar kasuwanci man wanda hakan ya kara habaka fannin na man.
Ya sanar da cewa, a yanzu kamfnin na NNPC, na gudanar da ayyukansa ne kai tsaye, ba tare da shishigin bangaren Gwamnatin Tarayya ba.
Mataimakin Shugaban kasar ya kuma jaddada mahimmancin gudunmawa kayan da ake sarrafawa a kasar suke da shi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasar.
Shettima ya sanar da cewa, ta hanyar dokar kayan da ake sarrafawa a cikin kasar nan ta 2010, Nijeriya ta samu damar kara shiga fannin samar da man fetur da iskar Gas wanda ya kai daga kashi 5 a cikin dari, zuwa kashi 30 a cikin dari.
Ya sanar da cewa, bisa nasarar da aka samu ta kafa matatar mai ta Dangote wacce kuma ta kasance mafi girma, a hakan ya sanya Nijeriya za ta iya kara mayar da hankali wajen sarafa kayan cikin gida.
Shi ma a na sa jawabin a wajen taron Mataimakin Shugaban kasar Côte d’Iboire, Tremoko Meyliet Kone, ya bayyana jin dadinsa kan ziyarar aikin da Shettima da sauran baki da suka halarci taron.