Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannun yarjejeniya da kungiyar tarayyar turayyar turai wato EU, da kuma gwamnatin kasar Jamus.
Sun kulla yarjejeniyar ce, domin a zuba Fam miliyan 17.9 a aikin babban layin wutar lantarki na kasar nan.
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 1.8 Ne Ke Fama Da Matsalar Yunwa – Hukumar FAO
- Harajin “VAT” Zai Kara Wa Al’ummar Kasar Nan Kuncin Rayuwa Ne Kawai – Gambo Danpass
An kaddamar da aikin ne, a karkashin shiri kashi na uku, na tallafwa fannin makamashi tare da samar da haske da kuma samar da wutar lantaki a karkara.
Shirin na EU, zai bai wa jama’a 154,000 samun wutar da kuma hada sauran mutane 30,000 domin su samu iskar Gas.
Kazalika, a kashi na uku, za a kuma samar da megawatt ta wuta guda takwas.
A 2013 ne, aka kaddamar da shirin wanda EU da ma’aikatar bunkasa tattalin arziki ta kasar Jamus, tare da hadaka da Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit da ma’a’ikatar kula da makamsshi, domin ya taimakawa Nijeriya
A jawabinta a wajen kaddamarwar da a wata ganawa dangane da shirin na NESP kashi na uku, shugabar sashen bunkasa tattalin arziki ta fasahar zamani a EU Inga Stefanowicz, ta yi nuni da cewa, domin a cimma burin yin kasuwanci na sahishi, aiki ne da ya rayata a kan kowanne mai ruwa da tsaki a fannin.
Inga wadda kuma ita ce ta jagoranci tawagar zuwa Nijeriya da zuwa kungiyar ECOWAS ta ce, EU ta jima ta na taimakawa Nijeriya domin ta cimma burinta na samar da tsaro a fannin samar da makamashi.
Ta kara da cewa, EU ta kuma taimakawa Nijeriya, a kan cimma burinta na ci gaba da wanzar da fannin makamashin ta, musamman wajen kara gwama yawan makamashin ta a fannin samar da wutar lantarki.
Ta ci gaba da cewa, a yayin da aka kadfdamar da wannan kashin na uku, a nan gaba za a kuma kaddamar da wasu, wanda ta ce, a wannan sabon shirin mutane 154,000 za su samu wutar lanrkin, inda kuma mutane 30,000, za su samu ingantacciyar iskar Gas na yin girgi na LPG.
Ta ce, akwai kuma tsarin kara samar da karin megawatt takwas ta makamashi tare da kafa hasken wuta na sola a cikin aikin kiwon lafiya.
Shi ma a na sa jawabin a wajen kaddamarwar mataimakin Jakadan kasar Jamsu Johannes Lehne, ya nanata kudurin gwamnatin Jamus na ci gaba da taimakawa Nijeriya, domin ta cimma burinta na aikin samar da makashi.
Ya bayyana cewa, shirin kashi na uku, ma’aikatar bunkasa tattalin arziki ta kasar Jamsu ce, ta kaddamar dashi awatan Mayun 2024, inda ta zuba Fam miliyan 8.9.
Ya kara da cewa, tun a baya, EU hukumar ta kuma kaddamar karin wata Fam miliyan 9, wanda hakan ya kara kasafin jaimmlar shirin, zuwa Fam miliyan 17.9.
Shi kuwa a na sa jawabin a wajen kaddamawar babban sakatare a ma’aikatar samar da wutar lantarki Mahmuda Mamman ya bayyana cewa, aikin zai taimaka, musamman domin a ciki gibin ‘yan Nijeriya miliyan 100, da har yanzu, ba su iya samun wutar lantarki.
Ya sanar da cewa, yin amfanin da makamashin zai rage kalubalen da aka fuskanta na rashin samun wutar lantarki a kasar, musamman a karkara.
Ya bayyana cewa, shirin kashi na uku, ya samu nasara ne, saboda yadda aka samu nasara a kashi na daya da kuma na biyu, na shirin.
A cewarsa, a kashi na daya da na biyun, an kara yawan wutar da ake turawa zuwa ga alumomin da ke a karkara.
Shi kuwa shugaban shirin na NESP, Duke Benjamin, ya bayyana cewa, an faro aikin ne a shekarar 2013, wanda kuma zai samar da wutar lantarki zuwa ga alumomin da ke zaune a karkara, idan aka sanya su a babban layin samar da wautar lantarki na k