• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

by Abubakar Abba and Sulaiman
5 months ago
IFAD

Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Gidauniyar Bunkasa Aikin Gona ta Kasa da Kasa (IFAD)na kokarin samar da wata manhajar zamani ga manoman Nijeriya, domin fara tantance su.

Hadakar, za ta bayar da damar yi wa manoman kasar nan rijista, wacce za ta bayar da damar gano kowanne manomi da gonakinsa da irin kasar noman da yake amfani da ita da kuma irin nau’in amfanin gonar da yake nomawa.

  • Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin
  • 2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

Haka zalika, za a shigo da sashen samar da bayanai da kuma hukumar da ke rajistar katin dan kasa (NIMC), domin gudanar da wannan aiki.

Manhajar za kuma ta sama wa manoman kasar damar samun kudade a matsayin rance ba tare da wani bata lokaci ba daga wajen gwamnati.

Kazalika, ana sa ran aikin zai tattaro daukacin manoman da ke kasar da kuma samun bayanan kafatanin manoman da ke jihohi 36 na wannan kasa, ciki har da babban birnin tarayyar Abuja.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

A jawabinsa a wajen taron kaddamar da tsarin tattaunawa kan shirin yin amfani da fashar zamani na samar da yin rjitsar ta manoman kasar (NDFR), wadda aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja, Babban Sakatare a Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Dakta Marcus Ogunbiyi, ya bayyana cewa; sabon tsarin zai taimaka matuka, wajen rage duk wani matsayi da manoman kasar suke ciki, musamman manoman da ba su mallaki wata gona ba.

“Za mu tabbatar mun yi rijistar sunayen manoman kasar da kuma gonakinsu, sannan kuma ba wai kawai yin rijistar ba, har da irin nau’in amfanin da suke nomawa da kuma nau’in irin kasar da ke gonakin nasu,” in ji Marcus.

Dakta Marcus ya kara da cewa, babu wata gona da ba ta da manomi, amma akwai manoma da dama da ba su mallaki gonaki ba.

“Idan mun yi wa manoman rijistar, za mu raba musu Kati kai tsaye da kuma wani Katin na manhajar zamani, domin a rika yin aiki da manoman kai tsaye ta yadda za a iya saurin gano kowane manomi a cikin sauki,” a cewar Marcus.

Ya ci gaba da cewa, hakan zai bayar da damar samun adana bayanansu kai tsaye da ya kunshi na sheda, musamman domin su rika samun taimakon daga wurin gwamnat da ya hada da samun rancen kudin yin noma.

Markus ya bayyana cewa, domin samun cin nasarar wannan aiki, Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abincii, ta dauki wasu matakai domin samun bayanan manoman kasar tare da adana bayannan nasu.

Ya ci gaba da cewa, guda daga cikin dabarun aikin shi ne, na yin hadaka da hukumar da ke rajistar katin dan kasa (NIMC), musamman domin wanzar da wannan aiki na yi wa manoman rijista da kuma tattara bayanansu, domin tabbatar da ganin kowane manomi, an sanya shi a cikin tsarin.

Ita kuwa a nata jawabin, Daraktar IFAD a kasar nan, Madam Dede Ahoefa Ekoue ta bayyana cewa, sashen samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, na alfaharin kasancewa cikin wannan sabon shirin.

“Gundunmawarmu ita ce, kokarin samun damar jawo sauran abokan hadaka na gwamnati da kuma masu kamfanoni masu zaman kansu, ta yadda za su zuba kudade tare, domin taimaka wa kokarin gwamnatin kasar, na yin rijistar manoman kasar,“ in ji Dede.

Madam Dede ta kara da cewa, koda-yake a baya, an yi irin wannan kokarin, amma ya kamata a ci gaba da wannan shirin, duba da muhimmancin da yake da shi.

“A yanzu, gwamnatin kasar ta samar mana da wata alkibla da kuma umartar daukacin masu ruwa da tsaki a fannin aikin noman kasar, domin a yi aiki tare,“ in ji ta.

Ta sanar da cewa, irin wannan aikin ne muke yi da sauran abokan hadaka kamar irin su; Bankin Raya Nahiyar Afrika, Hukumar Bunkasa Samar da Wadataccen Abinci, Bankin Duniya, Tarayyar Turai, Bankin Bunkasa Musulunci da kuma Gwamnatin Burtaniya.

Kazalika, ta sanar da cewa; babbin abin shi ne, ta hanyar yin aiki da kungiyoyin manoman kasar nan, domin su ne za su amfana da aikin.

Madam Dede ta ci gaba da cewa, hukumar ta IFAD, na matukar farin cikin jawo abokan hadaka da sauran sassan ma’aikatun gwamnati da sauran hukomomin gwamnatin kasar, domin tafiya tare cikin aikin.

Ta yi nuni da cewa, wannan aiki zai kasance tamkar samar da wani sauyi ne na ci gaba ga fanin aikin noman kasar.

Shi ma a nasa jawabin, Darakan kungiyar kasa da kasa ta Heifer da ke aiki a kasar nan, Dakta Lekan Tobe ya bayyana babban muhimancin da ke tattare da aikin, musamman ta hanyar yin hadaka.

Ya sanar da cewa, wannan aikin na daga cikin wasu shawarwarin da aka bayar a baya, wanda gwamnatin kasar nan ta yi hadaka da nufin yin amfani da fasahar zamani, domin a kara samar da wadataccen abinci a kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.