Yusuf Shuaibu" />

Gwamnatin Tarayya Na Da Kwarin Gwiwar Samun Haraji Mai Yawa A 2021

Ministar kudi da kasafi da tsare-tsaren kasa, Misis Zainab Ahmed ta bayyana cewa, bayan kudaden haraji da gwamnatin tarayya take tsammanin samu, tana kuma da gwarin gwiwar samun wasu kudaden shigan na musamman a shekarar 2021. Zainab ta bayyana hakan ne a wajen wani taro wanda ya gudana a faifan bidiyo a intanet a kan tattalin arziki, wanda kamfanin Delloite domin neman shawarwari yadda kamfanoni za su gudanar da harkokin kudade. Ministar ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da wasu manyan matakan shirin harkokin kudade guda biyu na farfado da haraji da kuma bunkasa tattalin arziki.

Ta kara da cewa, wadannan shiye-shirye za su kara inganta harajii wanda ya kai tsakanin kashi shida zuwa kashi 15 kafin shekarar 2023. Ta ce, za a samar da tsarin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi. Da take mayar da martani kan yadda za a gudanar da shirin wanda zai bayar da kashi biyu a cikin harkokin tattalin arziki cikin karamin lokaci, ministan ta bayyana cewa za a gudanar da taron mashawarta wanda zai bayar da damar kayyade yankunan da za a bunkasa. Ta ce, gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali ne a kan amsar haraji yadda ya kamata wanda zai bayar da damar samun kashi biyu a cikin harajin baya.
“Muna da dukkan hanyoyin da za mu bi wajen samun shawarwari a kan abubuwan da suka dace mu yi da wadanda ba su dace ba. Ina mai tabbatar muka ta cewa mun yanke shawarar za mu kara cibiyoyin a wannan gwamnatin da zai bamu damar samun kudade masu yawa,” in ji ta.
“Mun fahimci cewa hukumomin da ke tattara haraji ayyuka sun musu yawa wajen kayyade tabbacin harajin. Wannan ne ya sa muke kokarin dauke musu ayyukan kayyade harajin sai mu bar su da amsar harajin. Za su yi kokarin kayyade yawan masu amsar harajin da kuma hukumomin domin samun karin kashi biyu.
Zainab ta kara da cewa, gwamnatin tarayya tana aiki kafada da kafada da kamfanonin da ke Nijeriya wajen cimman wannan burin a shekaru biyar, yayin da take kokarin rage dogaro da mai.
“Muna da tafiya mai nisa amma ba mai wahala ba ce a majen mu. Wannan yawan dogaro da kanmu ba yanzu muka fara gudanarwa ba, mun fara ne tun a kan kasafin kudinmu wanda muke sammu daga mai , wanda mai da gas ne ke bunkasa tattalin arzikin Nijeriya a halin yanzu,” in ji ta.

Exit mobile version