Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, tana sa ran samun sama da Naira biliyan 300 a duk shekara a fannin noman Dabino.
Ta ayyana wannan kudiri nata ne, biyo bayan rabar da Irin Dabino na kimanin Naira miliyan biyar da ta yi, domin shuka shi a 2025.
- Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
- Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12
Darakta Janar na Hukumar Kula da Al’amuran da suka shafi Itatuwan Shukawa ta Kasa (NAGGW), Alhaji Saleh Abubakar, ya bayyana hakan yayin kaddamar da wani aikin shuke-shuke da hukumar ta gudanar a kauyen Maimalari da ke Karamar Hukumar Yusufari ta Jihar Yobe.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta kaddamar rabar da Irin Dabinon ne, miliyan biyar wanda take sa ran za a samar da Dabinon da ya kai kilo miliyan 500.
“Yana da matukar muhimmanci a sani cewa, wannan Iri na Dabino, kimanin miliyan biyar hukumar ta ce ta samar,” in ji shi.
Ya ce, za a rabar da Irin Dabinon ne a sauran jihohi sha daya da aka fi yin nomansa, musamman domin a kara habaka nomansa a wadannan jihohi.
“Kowane Irin Dabino daya a kasuwa, zai iya samar da akalla kilo 100 da kudinsa ya kai kimanin Naira miliyan daya, wanda kuma a duk shekara kowannensa za a iya yin nomansa sau biyu,” kamar yadda ya bayyana.
“Mun kiyasata cewa, manomansa da za su noma shi, zai samar wa da gwamnatin tarayya Naira 300, wanda hakan zai kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasar”.
Darakta Janar na Hukumar ta NAGGW ya bayyana cewa, manufar shirin ita ce, domin a kara karfafa bangaren tattalin arzikin kasar da kuma ci gaba da bayar da gudunmawar da bangaren ke yi na samar da sama da Naira biliyan 300 a sauran jihohin sha daya da ake nomansa.
Ya bayyana cewa, noman na Dabinon zai taimaka wajen habaka fannin ayyukan tattalin arzikin kasar da kuma kara kare fannin daga matsalolin sauyin yanayi da ke shafar fannin a jihar ta Yobe da kuma sauran jihohi sha daya da ake yin nomansa.
Daraka Janar ya kara da cewa, gangamin na shuka Itatuwan na daya daga cikin ayyukan hukumar na bikin hukumar na cika shekaru goma da kafuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp