Tsohon gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Malam Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin tarayya da zaɓar hanya biyan kuɗaɗe da samar da kayan tallafi ga ƴan bindiga ƙarƙashin abin da ake kira dabarar “non-kinetic” wajen yaƙi da rashin tsaro. Ya bayyana cewa wannan tsari ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro (ONSA) ne ke jagoranta, tare da jaddada cewa akwai hujjojin tabbatar da hakan.
A yayin tattaunawa a shirin Sunday Politics na gidan talabijin ɗin Channes, El-Rufai ya bayyana cewa gwamnati na bai wa ƴan bindiga kuɗi da kayan abinci, lamarin da ya kira “tallafa wa ta’addanci”. Ya ce ba zai taɓa amincewa da irin wannan dabarar ba. “Abin da ba zan taɓa yi ba shi ne in biya ƴan bindiga, in riƙa ba su tallafi na kudi da abinci da sunan hanyar magance ta’addan ba da ƙarfin Soji ba. Wannan wauta ce. Tamkar muna ƙarfafar su ne,” in ji shi.
- Ɗaukar Nauyin Ƴan Ta’addan Da Suka Farmake Mu A Kaduna Aka Yi – El-Rufai
- Ba Zan Nemi Kujerar Siyasa A 2027 Ba — El-Rufai
El-Rufai ya jaddada cewa wannan tsari ba ya fitowa daga gwamnatin Kaduna kai tsaye, sai dai daga Abuja. A cewarsa, “Ba gwamnatin Kaduna ba ce, manufar gwamnatin ƙasa ce da ONSA yasa gaba, kuma Kaduna na ciki. Jihohi da dama sun nuna rashin amincewa, amma wannan ce manufar yanzu — rungumar ƴan bindiga.”
Tsohon gwamnan, wanda ya daɗe yana fafutukar a yi amfani da ƙarfin Soji wajen murƙushe ƴan ta’adda, ya sake jaddada matsayinsa cewa “duk wani tubabben ɗan bindiga shi ne wanda aka kashe. Mu kashe su, mu buga da su, mu kawar da su baki ɗaya, sannan idan akwai kashi biyar cikin ɗari da suke son gyara, sai a taimaka musu. Ba za ka taba yin sulhu da maƙiya daga fuskar rauni ko tsoronsa ba, kuma ba za ka ba su kuɗi su je su sayi muggan makamai ba.”
Ya kuma yi gargaɗi cewa muddin wannan manufar biyan kuɗaɗen da neman sulhu da ƴan bindiga na ci gaba, matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya ba za ta gushe ba. El-Rufai ya kuma zargi gwamnatin Kaduna ta yanzu da gazawa wajen kare al’umma, yana mai cewa an riƙa biyan kuɗaɗen fansa masu yawan gaske a asirce. “Ni na yi gwamna shekaru takwas, makarantu uku kacal aka kai wa hari. Wannan gwamnati ta shafe shekaru biyu amma fiye da hakan aka kai wa hari. An biya biliyoyin Naira a matsayin kuɗin fansa. Idan gwamnati ko kowa zai musanta, muna da hujjoji, kuma zamu bayyana su lokacin da ya dace,”in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp