Gwamnatin tarayya ta amince da daga darajar filin Jirgin Sama na Muhammadu Buhari da ke Maiduguri zuwa matsayin filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa, tare da cikar shirin fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2025.
Ministan Sufurin Jiragen sama, Festus Keyamo, ne ya sanar da wannan ci gaba yayin da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umar Zulum, ya kai ziyara ofishinsa a Abuja.
- Ambaliya: Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Agaji A Borno
- Fasaha Da Balagar Harshen Manzon Allah (SAW) II
Keyamo ya jaddada muhimmancin wannan filin jirgin wajen haɗa yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman Jihar Borno, da ƙasashen waje, musamman daga Gabas ta tsakiya.
Gwamna Zulum ya bayyana gamsuwarsa da wannan ɗaga likkafa tare da yabawa gwamnatin tarayya bisa ƙoƙarin da take yi na canza yanayin harkokin sufuri na jiragen sama.
Haka kuma, ya yi kira ga kafa kamfanin jirgin saman ƙasa domin inganta hidima ga ‘yan Nijeriya. Wannan mataki ana ganin zai taimaka wajen buɗe damar haɓakar tattalin arzikin yankin.