Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya kaddamar da rabon kayan agaji ga wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ta Maiduguri ta shafa da ke fakewa a sansanoni kusan 36.
Ambaliyar ruwa ta afku a Maiduguri sakamakon ballewar madatsar ruwa ta Alau, wanda ya raba kusan mutane miliyan 2 da ke cikin birnin Maiduguri da kewaye da muhallansu.
- Ambaliya: Atiku Ya Bai Wa Jihar Borno Gudummawar Miliyan 100
- Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Miliyan 100 Ga Waɗanda Ambaliya Ta shafa A Borno
Kayayyakin tallafin sun hada da buhun shinkafa mai nauyin kilo 25, katon din taliya da tsabar kudi Naira 10,000.
Da yake zantawa da manema labarai, Zulum ya koka da cewa, mutane da dama da ambaliyar ruwan ba ta shafa ba na yin tururuwa zuwa sansanonin ‘yan gudun hijirar, wanda hakan zai iya kawo cikas ga aikin rabon kayayyakin cikin walwala.