Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Ba CBN Kashi 21 Na Jarinta Da Ke Kamfanin Buga Kudi

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta turawa Babban Bnakin Kasa CBN kashi ashirin da daya bisa dari na shiyar jarin ta dake kamfanin buga kudi. Mataimakain Shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda kuma shine shugaban cibyar sayara da hannun jari na kasa  a ranar talatar data gabata ce ya sanya ido a kan tura kudi wadda aka rattaba hannu tsa kanin Gwamnan Bankin Godwin Emefiele da kuma Darakta Janar na hukumar sayar da hannun jari na kasa Aled Okoh. An rattaba hannun ne a fadar shugahankasa dake Abuja. Kashi ashirin da dayar  na shiyar da aka turawa Bankin ya kai shiya ta naira biliyan 1.69. A jawabinsa a wurin sanya hannun Osinbajo ya bayyana cewar, kimanin kamfanoni 140 ne aka sanar za’a sayar da hnnun jarinsu a cikin shekaru talatin da suka wuce kuma gwamnati ta zuba kasha ashirin da dayar ne a matsayin jari don ta janyo ra’ayin masu son zuba jari daga bangaren gwamnmati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.Ya kara da cewar, Gwamnatin Tarayya ta sake zuba jarin ne a  NSPMC, inda ha kan zai taimaka wajen

kawo kwararru da za su ci gaba da tafiyar da Kamfanin. Yaci gaba da cewa CBN da abokin hadakar na De La Rue, wani kamfani mai zaman kansa sazu kawo dabaru ga NSPMC. Ya yi nuni da cewar fannin buga kudi a yanzu ya dauki wani sabon salo domin ya sha sabanain yadda aka sanshi a baya domin akwai wadanda a ayu suke ganin fannin fasaha ya riga ya mamaye fannininbda ya yi nuni da cewar idan ka kayi dubi a kan katinan da aka gurzawa  ayau, basu da wani tsada domin an gurza su ne ta hanyar fasaha a saboda da haka akwai  sababbin dabaru da a yau zamani yazo dasu.Osinbajo  ya kara da cewa, gwammanti za ta ci gaba da tabbatar da ana bin doka inda kuma kamfanoni masu zaman kansu suma za su tabuka wani abu. Shima a nasa jawabin  Gwamnan CBN Emefiele ya bayyana cewar NSPMC yana gurza ko Wacce irin takardar kudi ga ECOWAS. Ya kara da cewar karfin kamfanin ya karu domin a yanzu yana gurza kudaden da yake wadatar da kasar nan an kuma fadada kamfanin yadda zai samar da kudade da dama ga kasashen dake nahiyar Afirka. Acewarsa, muna kuma shirin kara jajircewa wajen fadada kasuwanci don sake samar da ababe masu amfani da masu ruwa da taski dak suke bukatar a gurza masu kudi. Ya bayyana cewar, a kan fannin takardun da suke neman tsaro muna yin aiki tukuru ganin cewar a baya gurza kudi a baya ana bukatar fasgo, biza dasuran wasu takardu da suke da mahimmancin gaske. Ya bayyana cewara a nan gaba kadan muna son muga NSPMC ya fara gurza fasgo ta hanyar kimiyyara zamani.Okoh ya kara da cewar hada-hadar ta sanya an samu samada naira biliyan sha bakwai ga asusun kasa kuma dabarun da CBN ta dauka sun taimakwa kamfanin matuka.Okoh  ya ce, gwamnatin tarayya ta mikawa CBN daukacin nasara da aka samu. Acewrsa, bayan da lokacin ya kare CBN ya nuna bukatarsa  na mallakar kamfanin, musamman idan akayi la’akari dayadda aikin kamafanin yake bukatar  sirri wanda ya hadada shige da fice da kuma kayan da za’a gudanar da gurza kudade. A karshe yace, bayan an gudar da dogon nazari a kan maganar Hukumar NPC ta yanke shawawr sayar da shiya kashi ashirin da daya bisa dari ga gwamantain tarayya ta hanyar bankin CBN inda za ta raike kashi 10.1bisa dari.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: