• English
  • Business News
Saturday, May 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci A Sama Wa Manoma Masu Renon Tsirrai Rancen Kudi

by Sadiq
55 minutes ago
in Noma Da Kiwo
0
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin tarayya ta bukaci cibiyoyin da ke bayar da rancen kudaden noma, da su kirikiro da tsarin da zai taimaka wa kananan manoma masu renon tsirrai, domin samar da tsirran masu tarin yawa a fadin wannan kasa.

Ministan Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wdataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya gabatar da wannan bukata a taron bita, domin samar da rance ga manoman da ke fannin renon tsirran.

  • ‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu
  • El-Rufai Ya Zargi Bangaren Shari’a Da Cin Hanci Da Rashawa

Kungiyar Masu Renonin Tsirrai ta Kasa (HortiNigeria) ce, ta shirya taron bisa hadaka da ‘HortiNigeria’ da hukumar bayar da bashin kayan noma, don habaka shi (NIRSAL) da aka gudanar a babban birnin tarayyar, Abuja.

“Muna da bukatar samar da rancen kudade ga manoman da ke wannan fanni, musamman kanana domin su zuba jarin na dogon zango a fannin”, in ji Kyari.

Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, renon tsirrai da kuma noman kayan Lambu, wani bangare ne da ke taimaka wa fannin aikin noman kasar.

Labarai Masu Nasaba

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi

Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

“Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi.

Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da Takin Zamni ta Kasa da Kasa (IFDC) da ke kasar nan, Dakta Yusuf Dramani ya bayyana cewa; cibiyar na aiki kafada da kafada da Hukumar NIRSAL, musamman don cike gibin da ake da shi a kasar, wajen samar da rancen kudaden noma ga manoman kasar.

“Duk da cewa, fannin aikin noma na kasar nan, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, amma abin takaici ne ganin yadda ake fuskantar kalubalen rashin samun rancen kudaden noma, musamman a fannin noman renon tsirrai.

“Mun yi amanna da cewa, za a iya sauya wadannan kalubalen da ake fuskanta na samar da rancen kudaden zuwa ga damarmaki, idan har cibiyoyin da ke bayar da rancen kudaden noman sun samar da kayan aikin da suka dace da ilimin da tsare-tsaren da suka kamata da sauransu,” in ji Yusuf.

Ya alakanta gudanar da taron da cewa, abu ne da ya zo kan gaba kuma mai muhimmancin gaske, wanda hakan zai bai wa cibiyoyin da suka halarci taron damar sanin yadda ake gudanar da hada-hadar kasuwanci a fannin na renon tsirrai da kuma irin dimbin damammakin da ke cikin fannin.

Shi kuwa, daraktan gudanar da shirye-shiye na kungiyar ta ‘HortiNigeria’ ta kasa, Mohammed Salasi Idris ya bayyana cewa, manufar da kungiyar ke son cimma, ita ce ta samar da damar samo rancen da ya kai kimanin Yuro miliyan 6, inda ya sanar da cewa, a yanzu mun kai sama da kashi 50 cikin 100 na wannan adadin kudi.

Da yake yin tsokaci kan kalubalen da ake fuskanta a fannin ya sanar da cewa, tsarin samar da rancen kudi na MPR da ke karkashin Babban Bankin Kasa (CBN), ya kara kudin ruwa na bayar da rancen kudin noma daga kashi 18 cikin 100 zuwa kashi 27 cikin 100, inda ya sanar da cewa; wannan babban kalubale ne ga wadanda suke fannin na renon tsirran.

Kazalika, ya sanar da cewa, wani karin kalubalen da manoman da ke Arewacin kasar nan ke fusanta shi ne, na tsadar biyan Leburori.

“Akasarin Leburorinmu, bisa rahotannin da muke samu shi ne, suna zuwa ne daga wasu iyakokin kasar nan, sannan kuma ga yadda darajar Naira ta fadi, inda ya kara da cewa; a cikin shekaru biyu zuwa uku, ba mu ji da dadi ba; musamman ganin yadda darajar Naira ta fadi warwas, kan takardar CFA, wanda hakan ya sa biyan aikin da Leburorin suka yi ya karu”, in ji Idris.

Shi kuwa, a nasa jawabin a wajen taron Jakadan Kasar Netherlands a Nijeriya, Bengt ban Loosdrecht, ya bayyana cewa; fannin na renon tsirrai na taimakawa wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasar da samar da aikin yi tare kuma da samar da abinci mai gina jiki.

Sai dai, Jakadan ya yi nuni da cewa; za a iya samun hakan ne, kawai idan aka samar da rancen kudade ga wadanda suke cikin fannin, wanda ita ce kadai mafita.

Bengt ban Loosdrecht, wanda Mista Folusho Adejoro, Mai Bayar da shawara a bangaren samar da wadataccen abinci da rage dumamar yanayi a ofishin Jakadancin kasar ta Netherlands a Nijeriya ya wakilce shi a wajen taron, ya bayyana cewa, manoma da dama a wannan fannin, na yin aiki tukuru, sai dai, suna fuskantar kalubalen samun rancen kudin renon na tsirrai.

Ya ci gaba da cewa, manufar taron shi ne, domin cike gibin da ake da shi na samar da damar samun rancen kudaden, wanda hakan zai bai wa bankuna da sauran cibiyoyin bayar da rancen kudaden noma fahimtar damar da ke cikin wannan fanni.

Ofishin Jakadanci na kasar ta Netherlands da ke kasar nan ce ke bayar da dauki a shirin habaka renonin tsirrai, wanda aka faro shirin tun a 2021 zuwa 2025, musaman domin tallafa wa fannin tare da samar da wadataccen abinci mai gina jiki a daukacin fadin Nijeriya baki-daya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: kuɗi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi

Related

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi

2 hours ago
Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci
Noma Da Kiwo

Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

1 week ago
Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu

2 weeks ago
Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

2 weeks ago
Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet
Noma Da Kiwo

Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet

2 weeks ago
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma
Noma Da Kiwo

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

2 weeks ago

LABARAI MASU NASABA

Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci A Sama Wa Manoma Masu Renon Tsirrai Rancen Kudi

May 24, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi

May 24, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Aikin Neman Man Fetur Arewacin Nijeriya — Ojulari

Za Mu Ci Gaba Da Aikin Neman Man Fetur Arewacin Nijeriya — Ojulari

May 24, 2025
Sin Ta Bukaci Kada Amurka Ta Siyasantar Da Hadin Gwiwar Bangaren Ilimi

Sin Ta Bukaci Kada Amurka Ta Siyasantar Da Hadin Gwiwar Bangaren Ilimi

May 23, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Sun Ci Gajiyar Tsarin Kasar Sin Na Samar Da Rangwamen Gwamnati Ta Musayar Sabbin Kayayyaki Da Tsofaffi

Kamfanoni Masu Jarin Waje Sun Ci Gajiyar Tsarin Kasar Sin Na Samar Da Rangwamen Gwamnati Ta Musayar Sabbin Kayayyaki Da Tsofaffi

May 23, 2025
Hukumar NPA Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci Da Rashawa Da Aka Lakaba Mata

Hukumar NPA Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci Da Rashawa Da Aka Lakaba Mata

May 23, 2025
Sin Da ASEAN Sun Kammala Tattaunawa Game Da Kafa Yankin Ciniki Cikin ‘Yanci

Sin Da ASEAN Sun Kammala Tattaunawa Game Da Kafa Yankin Ciniki Cikin ‘Yanci

May 23, 2025
An Gudanar Da Taron Kolin Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Na Duniya Na Shekara Ta 2025 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kolin Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Na Duniya Na Shekara Ta 2025 A Beijing

May 23, 2025
Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3

Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3

May 23, 2025
Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

May 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.