Babban Akanta Janar na Tarayya (AGF), Shamseldeen Babatunde Ogunjimi, ya bukaci masu gudanar da manhajojin lamuni a fadin Nijeriya, da su tabbatar da gaskiya, da rikon amana, da kuma nagarta wajen bayar da nagartaccen aiki ga ‘yan Nijeriya.
Ya bayar da wannan umarni ne a ranar Laraba a Abuja a ofishin babban Akanta-Janar na Tarayya (OAGF) a yayin bitar ayyukan masu ruwa da tsaki da ke bayar da lamunin kudi ga ‘yan Nijeriya.
Da yake kaddamar da bitar, AGF ya ce an shirya taron ne domin bitar ayyukan cibiyoyin da kuma sanar da shugabannin cibiyoyin sabbin sauye-sauye a tsarin tafiyar da hada-hadar kudi na Nijeriya.














