Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin kashi 4 na Free on Board (FOB) da Hukumar Haraji ta Nijeriya (NCS) ta sanya a kan duk kayan da ake shigowa da su. Shugaban Ma’aikatar Kuɗi kuma Ministan Hada-hadar Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ya bayyana wannan mataki bayan samun damuwa daga masu shigo da kaya, masana harkokin kasuwanci, da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antu game da illar harajin ga tattalin arziki.
A wata wasiƙa da aka sanya wa hannu ranar Litinin, 15 ga Satumban 2025, da aka aika wa Kwaturola Janar na Kwastam, Mista Wale Edun, a matsayinsa na Shugaban Kwamitin NCS, ya umurci dakatar da harajin nan take.
Wasiƙar da Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi kan Ayyuka na Musamman, Mista Raymond Omachi, ya
sanya wa hannu, ta bayyana cewa an gudanar da tattaunawa sosai da masu ruwa da tsaki da masana, inda
ra’ayinsu ya nuna cewa harajin zai kawo babbar matsala ga harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
- Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur
- Babu Shirin Gaggawa Wajen Fara Aiwatar Da Harajin Kashi 5 Na Man Fetur – Minista
“Bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki a masana’antu, masana harkokin kasuwanci, da
jami’an gwamnati masu dacewa suka yi, ya bayyana cewa aiwatar da wannan haraji zai haifar da manyan
ƙalubale ga sauƙaƙe harkokin kasuwanci, yanayin gudanar da harkokin kasuwanci, da kuma daidaiton
tattalin arziki gaba ɗaya,” in ji wasiƙar.
Masu ruwa da tsaki, musamman masu shigo da kaya da masu gudanar da kasuwanci, sun yi gargaɗi sau da yawa cewa harajin zai ƙara hauhawar farashi, ya sa kayan masarufi su yi tsada, kuma ya rage ƙarfin fafatawa na Nijeriya a kasuwannin duniya.
Da yawa kuma sun jayayya cewa wannan cajin zai ƙara wahalar da ƙoƙarin sauƙaƙe farashin gudanar da
kasuwanci a ƙasar.
A cewar ma’aikatar, dakatarwar ta na nufin samar da damar ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da
tsaki da kuma yin cikakkiyar bitar tsarin harajin da tasirinsa na dogon lokaci ga tattalin arziki.
A watan Afrilu 2025, Kwaturola Janar na Kwastom, Adeniyi, ya bayyana shirin sake gabatar da harajin
kashi 4 bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, cewa wannan cajin, wanda ake lissafawa bisa Free on
Board (FOB) na kayan da ake shigowa da su, an riga an sokƙ shi a baya daga al’umma masu kasuwanci
saboda nauyinsa ga masu shigo da kaya.
Nan da nan sanarwar ta jawo cece-kuce daga ƴ an kasuwa, kamfanonin jigilar kaya, da ƙungiyoyin
masana’antu, waɗanda suka bayyana cewa matakin zai rage amincewar masu zuba jari kuma ya rage jan
hankalin da Nijeriya ke yi a matsayin cibiyar kasuwanci.
Ma’aikatar kuɗi ta fayyace cewa dakatarwar ba ta nufin soke harajin, sai dai mataki ne na dakatarwa
domin sake duba yiwuwar tasirin harajin. Ma’aikatar ta jaddada ƙudurin gwamnati na daidaita samun
kuɗaɗen shiga tare da bunƙasa tattalin arziki.
“Ma’aikatar Kuɗi na sa ran yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumar Haraji ta Nijeriya (NCS) da duk masu
ruwa da tsaki domin shirya tsarin samun kuɗaɗe cikin adalci da inganci wanda zai tallafa wa kuɗaɗen
gwamnati ba tare da lalata harkokin kasuwanci ko daidaiton tattalin arziki ba,” in ji sanarwar.













