Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fara zagaye na biyu na Zauren Tattaunawa na Ministoci, inda Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Eshiokpekha Momoh, da Ƙaramin Ministan sa, Alhaji Uba Maigari Ahmadu, suka gabatar da jawabai kan ayyukan ma’aikatun su.
Da yake gabatar da jawabin maraba, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wannan zama da aka yi ranar Juma’a a matsayin dandalin da ke bajekolin nasarorin da Gwamnatin Tinubu ta cimma a fannoni daban-daban.
- KACCIMA Za Ta Baje Kolin Kayan Abincin Azumi Don Saukaka Wa Al’umma – Sidiya Gambo
- Saudiyya Za Ta Haramta Shan Giya Lokacin Gasar Kofin Duniya
Ya ce: “Ina maku maraba da zuwa zagaye na biyu na Zauren Tattaunawa na Ministoci na shekarar 2025. Kamar yadda kuka sani, a ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2025, na ƙaddamar da wannan jerin tarurruka na bana, inda na jaddada manyan nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.”
Ya ce Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi da ta Cigaban Yankuna suna daga cikin sababbin ma’aikatun da Shugaban Ƙasa Tinubu ya ƙirƙira domin bunƙasa fannin kiwo da haɓaka cigaban yankuna a Nijeriya.
Ya ce: “Waɗannan ma’aikatun guda biyu su ne sababbi a ƙasar. An kafa Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi a watan Yulin 2024 domin sauya damar kiwon dabbobi mai darajar biliyoyin daloli zuwa ingantaccen cigaban tattalin arziki ga ‘yan Nijeriya.
“Haka nan, an kafa Ma’aikatar Raya Yankuna a watan Oktoban 2024 domin kula da ayyukan hukumomin raya yankuna a faɗin ƙasar nan.
“Tun bayan kafuwar waɗannan ma’aikatun, ministocin sun fara aiki da himma, kuma sun zo a yau domin ƙarin bayani kan abin da suka aiwatar tun daga lokacin da aka ƙirƙiri ma’aikatun nasu.”
Ministan ya yaba da rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen yaɗa labaran zaman tattaunawar ministocin, yana mai cewa su ne ginshiƙin isar da sahihan bayanai ga ‘yan Nijeriya.
Ya kuma buƙaci ‘yan jarida da su guji yaɗa rahotannin da ke da ruɗani ko kwaskwarima.
Ya ce: “Kafofin watsa labarai sun kasance abokan hulɗar da ba za a iya musantawa ba a ƙoƙarin mu na ci gaba da sanar da ‘yan Nijeriya kan manyan nasarorin da Gwamnatin Tinubu ta cimma.
“Ina kira ga ‘yan jarida da su tabbatar da cewa rahotannin da suka shafi waɗannan tarurruka na bayar da bayanai ana gabatar da su da cikakken adalci da inganci.
“Bai kamata a riƙa cusa son rai ko ɓata gaskiya wajen rahoto kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati ba.
“Yana da kyau a samu sukar ra’ayi da bambancin fahimta domin dimokiraɗiyya, amma kada a bari ji-ta-ji-ta da karkatar da gaskiya su samu gurbi a muhawarar jama’a.”
Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yaɗa bayanan wannan zaman tattaunawar ta kafafen yaɗa labarai daban-daban domin tabbatar da gaskiya da karɓar ra’ayoyin jama’a.
Za a ci gaba da shirye-shiryen Zauren Tattaunawa na Ministocin, inda manyan jami’an gwamnati za su riƙa gabatar da bayanai kan cigaban da ake samu a fannoni daban-daban.