Ma’aikatar bunkasa kiwo ta hanyar cibiyar gudanar da bincken kula da lafiyar dabbobi ta kasa (NAPRI) da ke garin Shika, a Qaramar Hukumar Zaria a Jihar Kaduna, ta gabatar wasu nau’ika takwas na ciyar da Shanu da aka yi wa rijista, bayan aminta da su a shekaru 48 kan daukin da aka samar.
Wannan na kunshe ne, cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar, inda ta bayyana cewa; yin rijistar da kuma fitar da wadannan nau’ika takwas na ciyarwar ciyar da Shanu, wata babbar nasara ce ga ma’aikatar, musamman ganin cewa; ita ce ta farko bayan shekaru 48.
- Tsawa Ta Kashe Makiyayi Da Shanu A Kudancin Kaduna
- Sojoji Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu 32 A Katsina
Sanarwar ta ce, nau’ikan ciyawar, an mika su ga kwamiti na kasa da ke lura da nau’ikan ciyawa, domin yi wa nau’ikan rijista, sannan kuma a fitar da su.
A cewar sanarwar, nau’ikan ciyawar takwas, sun cimma matakin amincewa na cibiyar kula da jinsin ciyawa ta kasa, wato GRB da ke garin Ibadan, inda aka gabatarwa da cibiyar domin ta yi musu rijista a kuma fitar da nau’in ciyawar.
“Hakan ya kawo jimlar nau’ika guda dari na ciyawar da aka yi wa rijista a kasar, aka kuma fitar da su, musamman domin a kara bunkasa kiwon Shanu a kasar“, in ji Sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; yi wa nau’ikan ciyawar takwas rijista da kuma fitar da su, wani sabon sauyi ne kan samar da ciyawar ciyar da Shanun ciki, har da tsarin samar da ingantaccen Irin noma da kuma kara habaka bangaren kiwon dabbobi a kasar.
A cewar sanawar, hakan kuma zai kara taimakawa a bangaren zuba hannun jarin samar da abincin dabbobi da kara bunkasa kasuwancin abincin dabbobi da kuma kara fitar da abincin nasu, zuwa kasar waje.
Kazalika, ma’aiktar ta bayyana cewa, yi wa nau’ikan ciyawar takwas rijista da kuma amincewa da su, hakan zai taimaka wajen tabbatar da kara samar da ingantaccen Irin noma tsaftatacce wanda kuma hakan zai taimaka wa manoman kasar da masu kiwon dabbobi da kuma samar da kyakkyawan yanayi.
“Ingantaccen Irin noman da aka amince da shi ya kasance mai saurin nuna idan an shuka shi, wanda kuma ke jurewa dukkanin wani nau’ikan cututtukan da ke lalata Irin noma“, a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, hakan zai kuma kara taimakawa wajen kara samar da lafiyar ciyarwar, musamman wadda za ta taimaka wajen kara habaka kiwon dabbobi a dukkanin fadin wannan kasa.
Sanawar ta bayyana cewa, wannan amincewar da aka yi da Irin na noma, ya kai matsayin da ake bukata a hukumance, musamman domin tabbatar da an samar da zabin nau’ikan Irin noman da ake bukata.
A cewar sanarwar, hakan zai kuma taimaka matuka wajen kaucewa yin asara, sakamakon harbin cututtukan da ke kara habaka kasuwa da kara bunkasa zuba hannun jari da kare muhalli da sauran makamantansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp