Gwamnatin tarayya ta karbi ‘yan ci-rani 108 da suka makale a Jamhuriyar Nijar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Alexander Oturu, Ko’odinetan shiyyar Kudu maso Yamma na Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Muhalli ta Kasa (NCFRMI) ya fitar ranar Talata a Abuja.
- NFF Ta Sanar Da Ranar Fara Gasar ‘Federation Cup’ Ta Nijeriya
- Gwamnan Zamfara Zai Binciki Badakalar Miliyan 774 A Hukumar Alhazai Ta Jihar
Hukumar ta ce ‘yan Nijeriyar sun hada da maza 32, mata 29, yara 44 da jarirai uku.
“An iso da bakin hauren zuwa Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) suka kulla yarjejeniya ta bangarori uku na samar da matsuguni na wucin gadi ga wadanda aka dawo su.
Ofishin jakadancin Nijeriya da ke Yamai da IOM ne suka taimaka wajen dawo sa wadanda suka makale.
“A bisa tsarin da shugaban kasa ya zo sa shi, za a shigar da wadanda suka dawo cikin shirye-shiryen gwamnati da kuma shirye-shiryen Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp