Gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 101 ga cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 7,600 daga asusun samar da lafiya daga tushe (BHPF).
Dokta Chris Isokpunwu, sakataren kwamitin da ke sa ido kan ayyuka na ministoci, a ma’aikatar lafiya ne ya bayyana haka a Abuja, a wani taro na kwanaki biyu da kungiyar gyara harkokin kiwon lafiya (HSRC(, ta shirya.
- ‘Yansanda Sun Cafke Dan Damfara Da Katin Cirar Kudi 10 A AdamawaÂ
- Kurar Sauya Fasalin Kudi: ‘Mahaukatan’ Sayen-sayen Da Masu Boye Kudi Ke Yi
Taron bitar ya samu tallafi da ga Cibiyar Kasafin Lafiya ta Afirka (AHBN), da sauran abokan hulda.
Mista Isokpunwu ya ce an sakar wa BHCPF kudin dari bisa dari daga gwamnatin tarayya.
“Ya zuwa yanzu an raba kudaden ga cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko 7,600 a fadin kasar nan.
“Mun samu kudin da zai ishe mu rabo har zuwa Oktoba. Wannan ya kai kusan kashi 83 cikin 100 na kudaden da za a fitar a bana.
“Mun kuma samu ci gaba wajen yin rijistar adadin wadanda suka amfana da kuma bayar da kudade ga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko 7,600 a fadin kasar nan.
“Duk da cewa ba za mu dauki rajistar wadanda suka ci gajiyar tallafin ba ko kuma bayar da kudade ga cibiyoyin kiwon lafiya a matsayin nasara, mun yi imanin cewa mun fara ganin tasirin wannan kudade,” in ji shi.